Labarai
An Samar Da Sabon Tsari Da Zai Inganta Harkar Noman Rogo A Najeriya
Shugaban kungiyar masu noman rogo ta Najeriya (NCGA), Mustapha Othman Bakano, ya kaddamar da wani tsari na samar da kasuwa mai kyau da nufin karfafa wa manoman rogo da bunkasa harkar noma a Najeriya.
Alhaji Mustapha Othman Bakano ya bayyana bukatar samar da ingantattun hanyoyin kasuwanci don saukaka fitar da rogo kasuwannin ketare da kuma samar da kudaden musaya ga kasa.
Ya ce kungiyar na baiwa manoman da suka yi rajista da ita damar baje kolin kayayyakin amfanin gona da kuma cudanya da masu zuba jari na kasashen waje ba tare da wata matsala ba.
A karkashin sabon tsarin, Mustapha Bakano ya bayyana shirin samar da masana’antun sarrafa rogo a kowane yanki domin saukaka ayyuka da kuma bunkasa kasuwa ga manoma.

Baya ga samun kasuwa, shugaban kungiyar ya bayyana kokarin da ake yi na inganta dabarun noman rogo da rage lokacin girbi.
A cewarsa, ta hanyar bincike da ayyukan ci gaba, NCGA na kokarin inganta noman rogo domin wadata kasa da abinci.
Mustapha Bakano ya kara da cewa kungiyar za ta samar da dabarun kare manoma daga barazanar tsaro, inda za ta yi hadin gwiwa da jami’an tsaro domin kare lafiyarsu da kuma amfanin gona.
Hajazalika ya ce kungiyar za ta yi amfani da fasahar zamani wajen kare manoma daga fuskantar duk wata barazana ga amfanin gonarsu.
Ya ce a yanzu ya mayar da hankali ne wajen ganin an magance matsalar karancin abinci a jihar Kaduna da ma kasa baki daya, yana mai cewa zai kara jajircewa wajen yin amfani da kwarewarsa domin samar da ci gaba mai dorewa a fannin noma a Najeriya.
Umar S Fada
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
