Labarai
Isra’ila Tayi raga-raga da asibitin Al-shifa bayan samamen mako biyu

Rundunar sojojin Isra’ila ta ce ta janye daga asibitin al-Shifa da ke birnin Gaza bayan wani samame na tsawon mako biyu, wanda ya yi raga-raga da galibin gine-ginen asibitin.
A cewar rundunar tsaron sojin Isra’ila, dakarun ƙasar sun “hallaka ‘yan ta’adda” kuma sun gano “ɗumbin makamai da bayanan ayyukan sirri” a yankin.
Samamen ya faru ne bayan Isra’ila ta ce ta samu bayanan sirrin da ke nuna cewa Hamas na amfani da asibitin a matsayin wani sansanin ƙaddamar da hare-hare.
Hamas dai ta musanta amfani da cibiyoyin lafiya don gudanar da ayyukan sojoji.
A cikin ‘yan makonnin nan, an ba da rahoton ɓarkewar ƙazamin faɗa a zagayen asibitin, wanda shi ne mafi girma a Gaza.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
