Connect with us

Labarai

Mutumin da aka kashe wa duk ƴan’uwansa 103 a Gaza

Published

on

Ahmad al-Ghuferi ya tsira daga bam ɗin da ya kawar da iyalansa daga duniya.

Lokacin da wani hari ya hallaka iyalai da ƴan’uwansa su 103 a gidansu da ke Gaza, yana can maƙale a garin Jericho na Gaɓar Yamma, kimanin kilomita 80 daga gida.

Ahmad na aiki ne a wani wurin da ake aikin gini a Tel Aviv, lokacin da Hamas ta kai hari cikin Isra’ila a ranar bakwai ga watan Oktoba – ya kasa komawa gida wurin matarsa da ƴaƴansa mata uku sanadiyyar yaƙin da ya ɓarke da kuma rufe hanyar da sojojin Isra’ila suka yi.

A kullum akwai lokacin da suka ware shi da iyalansa domin yin waya da juna idan layin yana da kyau, kuma ko a lokacin da aka kai harin, yana kan waya tare da matarsa Shireen a ranar takwas ga watan Disamba.

Ya ce “Kamar ta san cewa za ta mutu, ta ce min na yafe mata kan duk wani abu maras kyau da ta taɓa yi min. Na ce mata ta daina irin wannan maganar. Amma wannan ce waya ta ƙarshe tsakaninmu.”

Wani mummunan harin bam da aka kai a gidan kawunsa a yammacin ranar ne ya hallaka matarsa da ƴaƴansa mata uku – Tala da Lana da kuma Najla.

Haka nan harin ya kashe mahaifiyar Ahmad, da ƴan’uwansa maza huɗu da iyalansu, da ƴan’uwan mahaifiyarsa da sauran dangi, su sama da 100.

Wata biyu bayan mummunan harin har yanzu gawawwakin wasu daga cikin su na maƙale a ƙarkashin gini.

A makon da ya gabata ne ya kamata ƴar’autarsa, Najla ta cika shekara biyu da haihuwa. Har yanzu Ahmad na fama da jimamin rashin iyalansa.

Kasancewar ba ya nan a lokacin da suka rasu da kuma lokacin da aka binne su, har yanzu Ahmad idan yana magana sai ya riƙa yi tamkar iyalan nasa na da rai, a wasu lokutan hawaye na kwarara daga idanunsa.

“Ƴaƴana su ne farin cikin raina,” in ji shi. “Ji nake kamar a mafarki. Har yanzu na kasa yarda cewa wannan lamarin ya faru.”

Ya goge hotunansu da ke wayarsa da komfutar tafi da gidanka saboda ka da abin da rinka damun sa.

An bar shi da haɗa labarin abun da ya faru daga abubuwan da makwabta da ƴan uwan da suka yi saura suka gaya masa.

Sun shaida masa cewa an harba makami mai linzami ne a ƙofar shiga gidan da iyalan nasa suke.

“Sun ruga da gudu suka shiga gidan wani kawuna da ke kusa, bayan mintoci 15 kuma sai wani jirgin yaƙi ya zo ya jefa bam a gidan. ” Ahmad ya bayyana.

Ginin mai hawa hudu da aka kashe iyalan nasa na kusa da wata kwana daga cibiyar lafiya ta Sahaba a birnin Zeitoun da ke Gaza.

Abun da ya rage yanzu sai tudun ƙasa da baraguzai da launin jini nan da can da yagaggun tufafi da kura ta buɗe.

Wata mota mai ruwan azurfa ta mokaɗe, gilashinta na gaba ya karkace kamar wadda ya yi haɗari, motar na ƙarƙashin wani bango da ke reto.

Wani ɗan’uwan Ahmad wanda ya tsira, Hamid al-Ghuferi, ya shaida wa BBC cewa a lokacin da aka fara kai harin, waɗanda suka gudu suka hau kan wani tudu su ne suka tsira, yayin da waɗanda suka ɓuya a cikin gidansu aka kashe.

“Ruwan wuta suka yi ta yi,” ya ce. “An kai hari kan wasu gidaje huɗu da ke kusa da namu, sun dinga jefa bam ne duk bayan mintoci 10.”

“Mutane 110 daga iyalan Ghuferi na gidan – yara da ƴan’uwa,” ya ce. ” Duka ban da ƙadan da suka yi saura duk sun mutu.”

Waɗanda suka tsira sun ce wadda ta fi kowa girma a cikin waɗanda suka mutu dattijuwa ce mai shekara 98, kuma mafi ƙanƙantarsu jariri ne da aka haife shi kwana tara kafin aukuwar harin.

Wani ɗan’uwa wanda shi ma sunansa Ahmad ya bayyana cewa abubuwa biyu ne suka fashe daga harin da aka kai ta sama.

“Kwatsam,” a cewarsa. “Idan ba don mutane sun riga sun bar wannan wurin ba, Ina ganin da kusan ɗaruruwa za a kashe. wurin sam ya sauya. Akwai wurin ajiyar motoci, wajen adana ruwa da gidaje uku baya ga wani ƙaton gida. Harin unguwa gaba ɗaya ya lalata. “

Hamid ya ce waɗanda suka tsira sun yi ta aikin tono gawarwaki daga baraguzai har asubahi.

“Jirage na shawagi a sama da kuma wasu jirage marasa matuƙa suna harbinmu a yayin da muke ƙoƙarin kaɗo su,” a cewar ɗan’uwan Ahmad.

“Muna zaune a gidan kawai sai muka tsinci kanmu a cikin baraguzai, ” Umm Ahmad al-Ghuferi ya shaida wa BBC. “An jefar da ni zuwa wani wuri. Ban san yadda aka fito da ni ba. Mun ga mutuwa muraran da idanunmu. “

Wata biyu da rabi har yanzu suna ƙoƙarin zaƙulo sauran gawarwakin daga ƙarƙashin baraguzai. Iyalan sun samu kuɗi suka yi hayar diga suna sassaƙar ginin.

“Mun gano gawarwaki huɗu [a yau],” Ahmad ya bayyana wa BBC, “Ciki har da matar ɗan’uwana da ɗan ɗan’uwana wanda aka ciro shi duk ya dagargaje. Sun kwashe kwana 75 a ƙarƙashin baraguzai.”

Kabuburansu na wucin-gadi na wani fili da ke kusa da nan, an yi musu sheda da sanduna da robobi.

Ahmad, wanda ke maƙale a Jericho, bai iya zuwa ya gan su ba.

“Mai na yi da za a raba ni da mahaifiyata da matata da ƴaƴana da ƴan’uwana? Yana tambaya “Dukanin su fararen hula ne.”

Mun tuntuɓi sojin Isra’ila game da zargin iyalan na cewa an hare su ne da wannan harin ta sama. Sai suka mayar da martani cewa ba su da masaniya kan wannan harin, kuma ma’aikatar tsaro ta (IDF) ta ce tana ɗaukar matakan da suka dace wajen rage kisan fararen hula a yaƙi da Hamas.

An yi gumurzu tsakanin sojin Isra’ila da mayaƙan Hamas a Shejaiyya, wanda ba shi da nisa ta kudanci da gidan al-Ghuferi, kwanaki kafin da kuma bayan kashe iyalan Ahmad.

A wasu bayanai da ake fitarwa kullum, a ranar tara ga watan Disamba, sojin sun ce sun “gano wasu ƴan ta’adda ɗauke da makamai masu linzami da ke lalata tankokin yaƙi” suna tunkarar dakaru a Shejaiyya, kuma suka kira jirgi mai saukar ungulu ya kai musu hari.

Rundunar ta kuma ce jiragen yaƙi sun kai hare-hare ta sama a wasu wuraren da suka ce ƴan ta’adda suke, yayin da suke ci-gaba da kai hari ta sama.

Yankin Zeitoun, inda gidan iyalan ya taɓa kasancewa, ya zama wani wurin da dakarun suka fi mayar da hankali wajen kai sabbin hare-haren sojin Isra’ila.

Ahmad na maƙale tare da mahaifinsa – wani magini a Gaɓar Yamma – Ahmad har yanzu yana kiran sauran ƴan’uwansa da suka rage a Gaza. Amma kasancewarsa a can na tsawon watanni, ba shi kuma da tabbacin ko zai taɓa komawa.

“An rusa duka burina a Gaza,” ya ce. “Wurin wa zan koma? Waye zai kira ni baba? Waye zai kirani masoyi? Matata tana gaya mini cewa ni ne rayuwarta. Wa zai gaya mini haka yanzu?”

Labarai

Labarai14 hours ago

Majalisar Dattijan Na So A Bai Wa Kananan Hukumomi Yancin Kai

Majalisar Dattijan Najeriya ta nemi Shugaba Tinubu ya shige gaba domin nema wa kananan hukumomi ‘yanci a wajen jihohi, wanda...

Labarai15 hours ago

‘Yan Ƙwadago Sun Yi Watsi Da N48,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

  Ƙungiyar Ƙwadago NLC ta yi fatali da tayin naira 48,000 da Gwamnatin Tarayya ta gabatar a matsayin mafi ƙarancin...

Labarai16 hours ago

Tinubu Zai Ciyo Bashin $500m Don Sayen Mitocin Lantarki

  Majalisar Dattawa ta sahale wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ciyo bashin Dala miliyan 500 da nufin samar da mitocin...

Ilimi17 hours ago

Za A Fara Daukar Masu Sakamakon Jarabawar NECO A Jami’o’in Birtaniya

  Jami’o’in kasar Birtaniya na shirin fara daukar daliban Najeriya masu shaidar jarabawar kammala sakandare ta NECO. Shugaban hukumar shirya...

Labarai2 days ago

Jirgin Farko Na Alhazan Najeriya Ya Tashi Zuwa Kasa Mai Tsarki

A yau Laraba 15 ga watan Mayun 2024 ne jirgin Najeriya na farko ya tashi da Alhazan Jihar Kebbi 423...

Labarai2 days ago

Najeriya Ta Kaddamar da Shafin Intanet Don Samun Bayanai Game da Ma’adinai

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shafin intanet ranar Talata wanda zai bai wa masu zuba jari damar samun cikakkun bayanai...

Labarai3 days ago

Tsohon Lauyan Trump Ya Ce Ubangidansa Ya Ba ‘Yar Fina-finan Batsa Toshiyar Baki

Tsohon babban lauyan Donald Trump, Michael Cohen, ya aikata abinda masu gabatar da kara su ka yi ta fatan ya...

Labarai3 days ago

Kotu Ta Yankewa Wani Mutum Hukuncin Zaman Gidan Yari Na Watanni 2 Bisa Satar Doya

Kotun Majistare da ke Gwagwalada a babban birnin tarayya Abuja, ta yanke wa wani mutum mai suna Isah Sani hukuncin...

Labarai3 days ago

Jamhuriyar Benin Ta Haramta Fitar Da Masara Zuwa Nijar

Jamhuriyar Benin ta hana fitar da masara zuwa ƙasashen waje a daidai lokacin da farashin hatsi ya yi tashin gwauron...

Labarai3 days ago

Gwamnatin Kano Ta Nada Ibrahim Garba Shugaban Tawagar ‘Yan Jarida A Hajjin Bana

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da nadin Ibrahim Garba Shuaibu a matsayin shugaban tawagar ‘yan jaridu a aikin Hajjin 2024....

Mafi Shahara