Labarai
An jikkata Yan jarida bakwai a wani hari a Gaza

Akalla ƴan jarida bakwai ne suka jikkata sakamakon hari ta sama da Isra’ila ta kai asibiti a tsakiyar Gaza.
Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta kai wa cibiyar bayar da umarni ta masu ikirarin jihadi da ke harabar asibitin al-Aqsa hari, inda ɗaruruwan mutane ke fake wa.
Mutane huɗu sun rasa rayukansu, ciki har da wani mutum guda da Isra’ila ta bayyana a matsayin kwamandan mayakan Jihadi.
A wani sabon labarin kuma, sojin Isra’ilan sun baje kolin makaman da suka ce sojojinsu sun kama a wani samame da suka kai asibitin al-Shifa da ke birnin Gaza, bayan zargin mayakan Hamas da ɓuya a cibiyoyin lafiya.
Jami’an lafiya a Falasɗinu sun ce mutane tara ne suka rasa rayukansu a harin da Isra’ila ta kai a Bani Suhaila da ke makwabtaka da Khan younis.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
