Labarai
Sojojin Najeriya sun tarwatsa sansanin IPOB a Imo
Rundunar sojin Najeriya tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro sun tartwatsa sansanin ƴan ƙungiyar IPOB da takwararta ta ESNda ke cikin dajin Ezioha a karamar hukumar Mbaitoli na jihar Imo.
Sojojin sun kai samame sansanin ne a ranar Alhamis, a wani yunkuri na kakkaɓe ƴan IPOB ɗin da kuma ƙawayesnu na ESN da ke iyaka da kogin Njaba da ke makwabtaka da al’ummar Awo-Omama a jihar ta Imo.
Yayin samamen, sojojin sun yi artabu da ɓata-garin, inda hakan ta sa suka tilasata wa wasu daga cikinsu tserewa zuwa cikin dazuka tare da munanan raunuka.
Sanarwa da sojojin suka fitar a shafin X, ta ce sun samu nasarar tono wasu abubuwan fashewa da aka binne da nufin hana sojoji kai wa wajen da ƴan IPOB ɗin suke.
Haka kuma, sun tono wasu gawawwakin wasu mutane da aka kashe bayan garkuwa da su, waɗanda aka binne a wasu ramuka a sansanin.
Sojojin sun ce za a je a gudanar da bincike kan gawawwakin kafin sake yi musu bizina ta ban-girma.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
