Labarai
Liverpool ta bi sahun Man Utd da Chelsea kan Neves

Liverpool ta bi sahun Manchester United da Chelsea a fafutukar neman sayen matashin danwasan tsakiya na Benfica Joao Neves, mai shekara 19, dan Portugal, wanda kwantiraginsa ya tanadi sayar da shi a kan yuro miliyan 120. (O Jogo, daga Sport Witness)
Manchester United da Manchester City kuma suna son sayen dan bayan Bayer Leverkusen, Jeremie Frimpong mai shekara 23, dan Netherlands. (Sun)
Sannan kuma Manchester Cityn na shirin sake zawarcin danwasan tsakiya na West Ham Lucas Paqueta na Brazil mai shekara 26 a bazaran nan. (Football Insider)
Ita kuwa Leeds United tana sa ran sake sayen tsohon danwasanta na tsakiya Kalvin Phillips na Ingila a kan kusan fam miliyan 30 daga Manchester City a bazaran nan idan har ta yi nasarar komawa gasar Premier. (Sun)
Kociyan Sporting Lisbon Ruben Amorim zai duba yuwuwar tafiya Liverpool idan aka ba shi aikin, to amma zai yanke shawara ne a karshen kakar nan. (Correio da Manha)
Newcastle za ta kara azama wajen neman babban dan baya a bazaran nan sannan kuma za ta sake bai wa dan bayanta Paul Dummett sabon kwantiragi bayan da kyaftin dinta Jamaal Lascelles ya tafi jinyar kusan wata tara ta gwiwa. (Newcastle Chronicle)
Tsohon kociyan Sheffield United Paul Heckingbottom ya zama na farko a jerin wadanda Sunderland da ke gasar Championship ke son dauka a matsayin mai horarwa na dindindin na gaba. (Sun)
A shirye Barcelona take ta saurari tayi a kan Raphinha a bazaran nan domin fita daga matsin rashin kudi a bazara, to amma kuma danwasan na Brazil ba ya son barin kungiyar. (Sport)
Tottenham za ta bayar da aron Alejo Veliz, 20, ga wata kungiyar daban a kaka mai zuwa, ganin cewa matashin na tawagar Argentina ta ‘yan kasa da shekara 20 ba a sa shi wasa sosai ba a zaman aron da yake yi yanzu a Sevilla. (Fabrizio Romano)
Tottenham ta bi sahun masu son matashin danwasan tsakiya na Leeds United Archie Gray, mai shekara 18 na tawagar Ingila ta ‘yan kasa da shekara 21, wanda kuma Liverpool ma na sonshi. (Football Insider)
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
