Connect with us

Labarai

Mutane Sama Da Miliyan 5 Ne Za Su Amfana Da Tallafin Abinci A Jigawa

Published

on

Gwamnatin jihar Jigawa ta kudiri  aniyar bada tallafin kayan abinci ga  mutane sama da  miliyan biyar a karkashin shirin ciyarwa  na watan Ramadan na bana.

Da yake jawabi a wajen kaddamar da rabon kayan abinci a karkashin shirin, gwamnan jihar Malam Umar Namadi ya ce gwamnatin jihar tana sane da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki, don haka ta fito da tsare tsare daban-daban a karkashin shirin ciyarwa na watan Ramadan.

Ya bayyana cewa, manufar shirin ciyarwa  a watan Ramadan ita ce domin a  taimaka wa al’umma su samu abin da za su ci yayin da suka yi Azumi.

 

Tun da farko, kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Auwalu Danladi Sankara ya bayyana cewa, za a raba buhunan shinkafa masu dauyin kilogiram 25 guda dubu dari daya da hamsin, sai na masara shima buhu dubu dari da hamsin, da katan din taliya guda dari  ga gidaje dubu dari da hamsin.

Gwamnan Malam Umar Namadi  ya amincewa  ma’aikatar ta samar da cibiyoyin  590 a karkashin  kwamitin shirin ciyarwa na watan Ramadan“.

A cewarsa, kowace mazaba gwamnatin jihar za ta kafa cibiyoyin bada tallafin guda biyu, tare da karin wasu cibiyoyi a masarautu biyar da wasu garuruwa.

Ya yi nuni da cewa,  kowace cibiya za ta  ciyar da mutane akalla 300 a kullum.

Ya ce, an kuma a samar da wani shiri na musamman na watan Ramadan ga ma’aikatan gwamnati, da jami’an tsaro, da  masarautu da sauran cibiyoyin gwamnati a jihar, a matsayin wani mataki na karramawa daga gwamna Umar Namadi.

Wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin da suka zanta da gidan rediyon Najeriya sun yabawa Gwamna Namadi bisa wannan karamcin.

Usman Muhammad Zaria

Labarai

Labarai3 days ago

Majalisar Dattijan Na So A Bai Wa Kananan Hukumomi Yancin Kai

Majalisar Dattijan Najeriya ta nemi Shugaba Tinubu ya shige gaba domin nema wa kananan hukumomi ‘yanci a wajen jihohi, wanda...

Labarai3 days ago

‘Yan Ƙwadago Sun Yi Watsi Da N48,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

  Ƙungiyar Ƙwadago NLC ta yi fatali da tayin naira 48,000 da Gwamnatin Tarayya ta gabatar a matsayin mafi ƙarancin...

Labarai3 days ago

Tinubu Zai Ciyo Bashin $500m Don Sayen Mitocin Lantarki

  Majalisar Dattawa ta sahale wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ciyo bashin Dala miliyan 500 da nufin samar da mitocin...

Ilimi3 days ago

Za A Fara Daukar Masu Sakamakon Jarabawar NECO A Jami’o’in Birtaniya

  Jami’o’in kasar Birtaniya na shirin fara daukar daliban Najeriya masu shaidar jarabawar kammala sakandare ta NECO. Shugaban hukumar shirya...

Labarai4 days ago

Jirgin Farko Na Alhazan Najeriya Ya Tashi Zuwa Kasa Mai Tsarki

A yau Laraba 15 ga watan Mayun 2024 ne jirgin Najeriya na farko ya tashi da Alhazan Jihar Kebbi 423...

Labarai4 days ago

Najeriya Ta Kaddamar da Shafin Intanet Don Samun Bayanai Game da Ma’adinai

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shafin intanet ranar Talata wanda zai bai wa masu zuba jari damar samun cikakkun bayanai...

Labarai5 days ago

Tsohon Lauyan Trump Ya Ce Ubangidansa Ya Ba ‘Yar Fina-finan Batsa Toshiyar Baki

Tsohon babban lauyan Donald Trump, Michael Cohen, ya aikata abinda masu gabatar da kara su ka yi ta fatan ya...

Labarai5 days ago

Kotu Ta Yankewa Wani Mutum Hukuncin Zaman Gidan Yari Na Watanni 2 Bisa Satar Doya

Kotun Majistare da ke Gwagwalada a babban birnin tarayya Abuja, ta yanke wa wani mutum mai suna Isah Sani hukuncin...

Labarai5 days ago

Jamhuriyar Benin Ta Haramta Fitar Da Masara Zuwa Nijar

Jamhuriyar Benin ta hana fitar da masara zuwa ƙasashen waje a daidai lokacin da farashin hatsi ya yi tashin gwauron...

Labarai5 days ago

Gwamnatin Kano Ta Nada Ibrahim Garba Shugaban Tawagar ‘Yan Jarida A Hajjin Bana

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da nadin Ibrahim Garba Shuaibu a matsayin shugaban tawagar ‘yan jaridu a aikin Hajjin 2024....

Mafi Shahara