Labarai
Sarkin Musulmi Ya Bukaci A Fara Duban Jinjirin Watan Ramadan
Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Saad Abubakar ya yi kira ga al’ummar Musulmin kasar nan da su fara neman ganin jinjirin watan Ramadan na shekarar 1445 bayan hijira, gobe Lahadi 10 ga Maris 2024 daidai da Kalandar Musulunci 29 ga watan Shaaban 1445 Hijira.
A wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addini da ke Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu ya ce, duk wanda ya ga jinjirin watan ya sanar da hakimi ko dagaci mafi kusa, domin tuntubar Sarkin Musulmi.
Za a iya amfani da lambobin waya da ke kasa don kai rahoton ganin jinjirin watan ga fadar Sarkin Musulmi.
08037157100
07067416900
08066303077
08036149757
08099945903
Daga Nasiru Malali
NASIR MALALI
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
