Labarai
Sarkin Musulmi Ya Bukaci A Fara Duban Sabon Jinjirin Wata A Gobe Talata
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ya yi kira ga al’ummar Musulmin kasar nan da su fara neman ganin jinjirin watan Rajab a gobe Talata 31 ga watan Disamban 2024, daidai da kalandar Musulunci 29 ga watan Jumada Thani Hijira ta 1446.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addinin musulunci na jihar Sokoto Farfesa Sambo Wali Junaidu, kuma Wazirin Sokoto, ya ce idan an gani sai a sanar ga gunduma ko kauye mafi kusa domin sanar da Sarkin Musulmi.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, duban wata yana fayyace kalandar Musulunci a cikin shekara guda, wanda hakan ya sa ganin watan Ramadan ya fi karbuwa ga al’ummar Musulmin kasar baki daya.
Daga Nasiru Malali
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
