Labarai
Shugaba Tinubu Ya Bayyana Alhininsa Bisa Rasuwar Tsohon Shugaban Amurka Jimmy Carter
Shugaba Bola Tinubu ya mika sakon ta’aziyyarsa ga gwamnati da al’ummar Amurka bisa rasuwar tsohon shugaban kasar Jimmy Carter, wanda ya rasu yana da shekaru 100 a duniya.
Jimmy Carter, wanda shi ne shugaban Amurka na 39, ya kasance hidimtawa al’ummasa, yana nuna wa shugabannin duniya babban tasirin sadaukarwa maimakon tunkaho da matsayin da mutum ya samu.
A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai da dabaru Bayo Onanuga ya fitar, ya ce a matsayinsa na wanda ya lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel kuma jigo a duniya, shugaba Carter ya sadaukar da rayuwarsa bayan shugabancin kasar wajen samar da zaman lafiya, dimokuradiyya, da kawar da munanan cututtuka. Yunkurinsa na ci gaba da gudanar da ayyukan alkhairi ya sanya duniya ba za ta taba mantawa da shi ba.
Shugaba Tinubu cikin shauki, ya tuna da Shugaba Carter a matsayin amintacce, kuma mai tausayi ga Najeriya. Ya yaba da irin gudunmawar da Carter ya bayar ta hanyar Cibiyar Carter, musamman kokarinsa na kawar da cutar kurkunu da sauran cututtuka a Najeriya, wadan hakan ya inganta rayuwar ‘yan Najeriya da dama.
Da yake jawabi kan dangantakar da ke tsakanin Najeriya da Amurka kuwa, Shugaba Tinubu ya tuna da ziyara mai cike da dimbin tarihi da Shugaba Carter ya kawo Najeriya a watan Maris na 1978, da kuma zamansa na kwanaki uku a gidan gwamnati da ke Marina, jihar Legas. Karkashin jagorancin Carter, wannan ziyarar ta kasance wani muhimmin lokaci a manufofin harkokin wajen Amurka. Ya aza harsashin kulla kyakkyawar alaka tsakanin Amurka da Afirka, tare da fifita Najeriya a matsayin cibiyar Afirka.
Daga Bello Wakili
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
