Labarai
‘Yan Sanda Sun Ceto Dan Kasar Sin Da Aka yi Garkuwa Da Shi A Kwara
Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta ceto wani dan kasar Sin wato China ami suna PengChao Zhang da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi a Eiyenkorin da ke karamar hukumar Asa ta jihar.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan DSP Ejire-Adeyemi Toun ya fitar, ya ce wasu ‘yan bindiga shidda sun yi garkuwa da Mista PengChao Zhang, wanda aka fi sani da Williams Kaka a lokacin da yake da abokan kasuwancinsa da a wani massukin baki a ranar 10 ga Maris, 2024.
Sanarwar ta ce, rundunar da ‘yan tare da hadin gwiwar jami’an sa kai sun aiwatar da jerin bincike da suka kai ga ceto dan kasarSin din.
Sanarwar ta bayyana cewa, tuni aka sada shi da iyalansa ba tare da wani rauni ba.
Ta kara da cewa, wannan nasara da aka samu na nuna jajircewar rundunar ‘yan sandan jihar wajen tabbatar da tsaro ga dukkan mazauna jihar da maziyartan jihar.
Rundunar ‘yan sandan ta kum bukaci jama’a da su sanya ido tare da kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba ga jami’an tsaro domin daukar matakin gaggawa.
Ali Muhammad Rabi’u
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai21 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai23 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
