Labarai
Matatar Man Ɗangote Ta Fara Sayar Da Man Jirgi Da Na Dizil
Matatar man attajirin Najeriya Aliko Dangote ta fara fitar da albarkatun man fetur din da ta tace, kamar yadda daya daga cikin manyan jami’an kula da matatar da kuma kungiyar dillalan man fetur din a Najeriya suka tabbatar.
Daga cikin manyan jami’ai a rukunonin kamfanin na Dangote Devakumar Edwin ne ya tabbatar da samun wannan ci gaba, yayin zantawa kamfanin dillancin labarai na Reuters, inda ya ce tuni suka fara rarraba wa ‘yan kasuwa man disel da kuma man jiragen sama.
A cewar jami’in, litar mai miliyan 37 suke fatan cimma fara dorawa manyan jiragen ruwa, amma a halin yanzu suna iya lodin litar man miliyan 26.
Kamfanin dillancin labaran na Reuters ya kuma ruwaito shugaban kungiyar dillalan man fetur na Najeriya Abubakar Maigandi na cewa, sun cimma matsayar sayen litar man disel daga matatar man ta Dangote kan farashin naira dubu 1,225, kwatankwacin kusan dalar Amurka guda, wanda za su rarraba zuwa sassan Najeriya.
Matatar man ta Dangote da ke jihar Legas ta lakume dalar Amurka biliyan 20 kafin kammala aikin gininta, wadda za ta rika tace gangar danyen mai dubu 650,000 a kowace rana, abinda yasa idan har ta fara cikakken aikin da aka tsara mata a bana ko kuma badi, matatar za ta zama mafi girma a nahiyar Afirka da ma Turai, ci gaban da ake fatan zai kawo karshe ko kuma rage dogaron da Najeriya ke yi wajen shigar da tataccen man fetur daga Turai, duk da dimbin arzikin danyen man da take da shi.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
