Labarai
Mutane 7 Sun Mutu Sanadiyar Girgizar Kasa A Taiwan
Akalla mutane 7 ne suka mutu a girgizar kasa mafi muni ta baya-bayan da aka samu cikin shekaru 25 a Taiwan, sannan akwai wasu sama da dari 7 da suka samu raunuka.
Hukumomin kasar sun ce, jami’an bada agaji na ci gaba da aikin ceto wadanda suka makale a cikin gidaje da dama da lamarin ya shafa.

A cewar wani malamin asibiti a Taipei, Chang Yu-lin, girgizar kasar mai karfin maki 7 da 2, ta afkawa yankin Gabashin kasar ne da ke da yawan jama’a.
Girgizar da aka sameta a nisan kilomita 15.5, ta faru ne a dai-dai lokacin da mutane ke tafiya aiki da zuwa makaranta, wacce kuma ta haifar da baraznar tasowar Tsunami a kudancin Japan da kuma Philippings, duk da cewa daga baya an ce ta kauce.
Jami’an kashe gobara sun ce har yanzu akwai kimanin mutane 60 daga cikin kusan 77 da suka makale a hanyoyin karkashin kasa da ke arewacin birnin Haulien.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
