Labarai
Gwamnatin Tarayya Ta Kara Kudi Ga Wadanda Suka Fi Samun Wutar Lantarki
Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya ta amince da karin kudin wutar lantarki da ‘yan kasar ke biya karkashin rukunin A wanda ya fara aiki daga wannan Larabar.
Mataimakin shugaban hukumar, Musliu Oseni ya shaida wa taron manema labarai a birnin Abuja cewa, a karshin wannan sabon karin, wadanda suke rukunin ‘A’ za su rika biyan naira 225 na kilowatt cikin sa’a guda, sabanin naira 66 da suka saba biya kafin sabon tsarin.
Wadanda ke karkashin rukunin ‘A’, na shan wutar lantarki na tsawon sa’o’i 20 a kullum.
Oseni ya ce, wannan rukuni na wakiltar kashi 15 na mutanen da ke biyan kudi don shan wutar lantarkin a Najeriya.
Babban jami’in na Hukumar Kula da Wutar Lantarkin ya kara da cewa, sun kuma mayar da wasu zuwa rukunin B daga rukunin A na masu shan wutar lantarkin, saboda rashin ba su wutar na tsawon sa’o’i 20 a kowacce rana.
Sai dai jami’n ya ce, sabon tsarin karin kudin ba zai shafi wadanda ke samun wutar lantarkin a karkashin sauran rukunnan da ake da su a kasar ba.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
