Labarai
Ma’aikatan Ceto Na Cigaba Da Neman Jirgin Shugaban Kasar Iran Da Ya Bace
Da yammacin yau lahadi ne tarin ma’aikatan ceto suka bazama wajen aiki gano jirgi mai saukar ungulu dauke da shugaba Ebrahim Raïsi na Iran, wanda wani “hatsari” ya rutsa da shi, kamar yadda jami’ai da kafafen yada labaran kasar suka sanar.
An kaddamar da bincike don gano jirgin mai saukar ungulu amma ya yi wuya saboda “yanayi mara kyau”, ciki har da hazo, in ji ministan cikin gida Ahmed Vahidi a gidan talabijin na kasar.
Jirgin na shugaba Raïsi na daya daga cikin ayarin jirage masu saukar ungulu uku dauke da tawagar shugaban kasar.
“Zai iya ɗaukar lokaci kafin a isa yankin da wannan jirgi ya fadi ,” in ji ministan cikin gida Ahmed Vahidi, kodayake wannan wurin zai kasance a cikin dajin Dizmar, kusa da garin Varzaghan.
Ebrahim Raïssi ya ziyarci lardin gabashin Azarbaijan a yau lahadi, inda ya kaddamar da wata madatsar ruwa tare da shugaban kasar Azarbaijan Ilham Aliev a kan iyakar kasashen biyu.
Raïssi, mai shekaru 63 , ya kasance shugaban Jamhuriyar Iran tun watan Yunin 2021.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
