Labarai
Trump Ya Aike da Daftarin Shirin Zaman Lafiya ga Iran
Shugaban Amurka Donald Trump ya aike wa Iran wani daftarin shirin zaman lafiya, inda ya bayyana ƙwarin gwiwar kawo ƙarshen yaƙin da aka shafe kusan wata guda ana gwabzawa, a yayin da Iran ta sanar da cewa za ta bai wa jiragen waɗanda ba sa gaba da ita damar wucewa ta mashigar ruwan Hormuz.
Wannan alama ta kawo ƙarshen yaƙin da ake gwabzawa ta hanyar diflomasiyya na zuwa ne duk kuwa da sabbin hare-hare da ɓangarorin da ke kai ruwa rana ke kwarara wa juna, lamarin da ke cigaba da haddasa ta’adi ga dukkaninsu.
Trump, wanda kalamansa a cikin ƴan kwanakin nan suka tashi daga shan alwashin munanan hare-hare akan Iran, zuwa ayyana cewa yaƙin na daf da kawo ƙarshe, ya ce Amurka na cikin tattaunawa a halin da ake ciki, sai dai Iran ba ta tabbatar da hakan ba.
Shugaban Amurkan ya shaida wa manema labarai a Washington cewa Iran ta ɗauki wani mataki da ya burge su, lamarin da ke nuni da cewa su na tattaunawa da waɗanda suka kamata, sai dai bai yi wani ƙarin bayani akan wannan furuci ba.
Jim kaɗan bayan kalaman Trump ne Iran ta cikin wani saƙo da hukumar kula da sufurin ruwa na ƙasa da ƙasa ta yaɗa, ta ce ta bai wa jiragen ƙasashen da ba sa rigima da su damar wucewa mashigar ruwan Hormuz lafiya.
Tun da farko a cikin ‘ƴan kwanakin da suka wuce, Iran ta ce ba ta rikici da ƙasashen da ke kyautata mata, sai dai duk da haka jiragen ruwa da dama sun dakatar da bin hanyar, duba da yadda kamfanonin inshora suka kauce wa ɗaukar kasada.
rfi
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
