Labarai
Hukumar Lafiya a Kano ta Shirya Taron Masu Ruwa da Tsaki Kan Cutar Shan Inna
Daga Khadijah Aliyu
Hukumar Kula da Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Kano (KSPHCMB) ta gudanar da wani muhimmin taron game da shirye-shiryen tunkarar gamgamin wayar da kai kan allurar rigakafin cutar shan inna na watan Maris, a wani bangare na kokarin ci gaba da tabbatar da jihar ba ta da cutar tare da karfafa harkokin rigakafi na yau da kullum.
Taron, wanda aka gudanar a Cibiyar Ayyukan Gaggawa (EOC), ya hada manyan masu ruwa da tsaki, abokan hulda, da jami’an lafiya domin daidaita tsare-tsare da kuma karfafa hadin kai gabanin gudanar da shirin.
Yayin da yake jagorantar taron, Darakta Janar na KSPHCMB, Farfesa Salisu Ibrahim, ya jaddada muhimmancin hadin kai, da kuma sa hannun al’umma wajen tabbatar da nasarar shirin.
Ya bayyana cewa samun kyakkyawan sakamako na bukatar cikakken hadin gwiwa tsakanin dukkan bangarorin da ke da hannu a ayyukan rigakafi a fadin jihar.

Farfesa Ibrahim ya kuma jaddada bukatar fayyace ayyuka da nauyin da ya rataya a wuyan kowane bangare, ciki har da masu unguwanni, ma’aikatan lafiya, da sauran abokan hulda.
Ya ce hakan zai kara inganta gudanar da ayyuka tare da tabbatar da an kai ga jama’a da dama.
An kuma mai da hankali musamman kan rawar da Jami’an Rigakafi na Kananan Hukumomi (LIOs), Wakilan Unguwanni, Masu Ba da Shawara na Rukunoni, da Masu Sa-kai za su taka, musamman a fannonin wayar da kai, yin allurar rigakafi, da sa ido a matakin kasa.
Hukumar ta sake jaddada kudirinta na gudanar da ingantaccen shirin rigakafi mai tasiri ta hanyar karfafa hadin gwiwa da ci gaba da hada kan al’umma.
An kuma bukaci masu ruwa da tsaki da su kara kaimi wajen wayar da kai, tare da yin aiki tare domin tabbatar da cewa kowane yaro da ya cancanta ya samu allurar rigakafi.
Shirin watan Maris na daga cikin ci gaba da kokarin kawar da cutar shan inna da kuma inganta sakamakon rigakafi na yau da kullum a Jihar Kano.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
