Labarai
Iran ta yi jana’izar kwamandojin sojinta da masana nukiliya waɗanda Isra’ila ta kashe
Iran ta gudanar da jana’izar mutum 60, ciki har da kwamandojin sojinta da masana nukiliya da Isra’ila ta kashe a kwana 12 da suka yi suka gwabza yaƙi.
An gudanar da jana’izar ce ta karramawa, inda aka lulluɓe gawarwakinsu da tutar Iran, sannan dandazon mutane suka halarta sanye da baƙaƙen kaya domin jimami da kuma karrama waɗanda suka rasun.
A farkon makon ne aka kawo ƙarshen yaƙin ta hanyar shiga yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin ƙasashen biyu bayan Amurka ta shiga tsakani.
Amurka ta kai hare-hare ne a cibiyoyin nukiliyar Iran, inda ta sanar da cewa ta samu nasarar tarwatsa cibiyoyin, waɗanda dama a kansu ake yaƙin.
Daga cikin waɗanda aka binne akwai Mohammed Bagheri, wanda babban hafsan soji ne a ƙasar ta Iran, kuma shugaban ma’aikata a rundunar sojin ƙasar.
Akwai kuma Hossein Salami, wanda kwamandan dakarun juyin juya-hali ne na Iran, da masanin nukiliyar ƙasar Mohammad Mehdi Tehranchi.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
