Labarai
“Gwamnatin Tarayya Karfafa Sashen Kiwon Lafiya Don Takaita Fitar Wajen Nijeriya Neman Magani
Gwamnatin tarayya na aiki tukuru don hana zuwa kasashjen wajen Neman ta hanyar karfafa tsarin kiwon lafiyar kasar.
Rajistara Hukumar Kula da Lafiya ta Al’umma ta Najeriya, Dokta Bashir Idris Lifidin Jama’a ya bayyana haka a wani taron da ma’aikatan hukumar suka shirya domin murnar sake nada shi da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya yi a Abuja.
Ya yi nuni da cewa fitar ‘yan Nijeriya kasashen waje neman lafiya kalubale ne da ke shafar tsarin kiwon lafiya, amma ya bayyana fatan gwamnatin tarayya na tsara hanyoyin da za ta magance shi.
Dokta Bashir Idris ya bayar da shawarar tura karin kayan aiki da kuma ma’aikata don hana likitoci da ma’aikatan jinya zuwa kasashen ketare don samun gwaggwaban aiki.
Ya kuma ba da tabbacin cewa hukumar za ta ci gaba da bayar da gudummawar kasonta domin tunkarar kalubalen da harkar kiwon lafiya ke fuskanta, duba da kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na inganta harkar kiwon lafiya a kasar nan.
A nasa jawabin, tsohon dan majalisar tarayya mai wakiltar kudancin jihar Kaduna, Sanata Danjuma La’ah ya yabawa magatakardar hukumar Dakta Bashir Idris Lifidin Jama’a bisa jajircewarsa wajen yin tasiri ga dimbin rayuka a fadin kasar nan tun bayan hawansa mulki.
Maryam Idris
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
