Labarai
Jigawa: Dubban Mahaddata Sun Halarci Taron Addu’o’in Zaman lafiya ga Najeriya
Gwamnatin Jihar Jigawa ta gudanar da addu’o’i na musamman domin samun zaman lafiya mai ɗorewa, ingantaccen tsaro da ƙarfafa haɗin kan al’amurar Najeriya.
An gudanar da taron ne a Cibiyar Horar da Ma’aikata ta Manpower Development Institute da ke Dutse, inda dubban mahaddata Al-Qur’ani da malaman addinin Musulunci daga sassa daban-daban na ƙasa suka halarta, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Umar Namadi.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Umar Namadi ya ce an shirya zaman addu’ar ne a matsayin wani ɓangare na tallafawa kokarin da gwamnatoci a matakai daban-daban ke aiwatarwa domin magance matsalolin tsaro da sauran ƙalubalen da ƙasa ke fuskanta.
Ya jaddada cewa baya ga tsare-tsare da ayyukan jami’an tsaro, ƙorfafa ibada da addu’o’i su ne kan gaba wajen neman zaman lafiya da kwanciyar hankali mai ɗorewa.
Malam Umar Namadi ya ƙara da cewa Gwamnatin Jihar Jigawa ce tare da Cibiyar Ƙasa ta Mahaddatan Al-Qur’ani da kuma Ƙungiyar Mahaddatan Al-Qur’ani ta Jihar Jigawa suka haɗa hannu wajen shirya shirin.
A cewarsa, mahalarta daga jihohi kusan 26 na ƙasar nan ne suka halarci shirin, inda mahaddatan suka yi fiye da khatma 4,000 na Al-Qur’ani, tare da gudanar da addu’o’i na musamman domin zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban Najeriya.
Namadi ya bayyana cewa taron addu’ar ya zo daidai da kwanaki goma na farkon watan Zul-Hijjah, wanda lokaci ne mai muhimmanci a addinin Musulunci, yana mai bayyana fatan cewa addu’o’in da aka yi za su jawo rahama da albarkar Allah SWT.
Ya ce: “Mun zaɓi kwanaki goma na farkon Zul-Hijjah saboda falalar da suke da ita, tare da fatan In Shaa Allah za a sami zaman lafiyamai dorewa.”
Ya ƙara da cewa an kuma shirya shirin ne domin tallafawa ƙoƙarin gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu wajen yaƙi da rashin tsaro, ƙarfafa haɗin kan ƙasa da bunƙasa ci gaban tattalin arziki.
Gwamnan ya yabawa wadanda suka shirya taron, malaman addini da mahalarta bisa jajircewarsu da sadaukarwarsu, yana mai bayyana taron a matsayin wata alama ta kishin ƙasa da damuwa da makomar Najeriya.
Ya kuma buƙaci ‘yan Najeriya su ci gaba da yi wa ƙasa addu’a tare da goyon bayan shirye-shiryen gwamnati da ke da nufin samar da zaman lafiya da ci gaba.
Taron ya ƙunshi karatun Al-Qur’ani, addu’o’in zaman lafiya da tsaro, da kuma addu’o’i na musamman ga shugabannin ƙasa, jami’an tsaro da al’ummar Najeriya baki ɗaya.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
