Connect with us

Labarai

Zulum Ya Kaddamar Da Rabon Kayan Abinci Ga Iyalai Dubu Dari

Published

on

 

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya kaddamar da rabon kayan abinci ga iyalai musu rauni sama da dubu dari daya a kananan hukumomin Maiduguri  da Jere.

 

An yi rabon ne da nufin rage wahalhalun  tsadar kayan abinci da sauran muhimman kayayyakin amfanin yau da kullun.

 

A jawabinsa yayin kaddamar da rabon kayayyakin a cibiyar wasanni ta Maiduguri, Gwamna Zulum ya ce kowane gida zai sami buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 25 da buhun masara shi ma mai nauyin kilogiram 25.

 

Ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa ta ba da fifiko ga jin dadi da walwalar jama’a, musamman wadanda rikicin Boko Haram ya shafa.

Mun kaddamar da rabon kayan abinci ga magidanta dubu dari ne daga birnin  Maiduguri da kewaye. Kowa a Najeriya ya san irin wahalhalun da mutane ke fuskanta dangane da karancin abinci,” In ji Zulum.

 

A cewar Gwamnan, za a raba kayayyakin ne ga masu karamin karfi a cikin al’umma domin rage radadin tsadar rayuwa da ake fuskanta.

 

Gwamnan ya kuma bayyana cewa za a kara yawan rabon tallafin daga iyalai dubu dari zuwa sama da iyalai dubu dari biyu a kananan hukumomi bakwai dake kudancin jihar kafin karshen azumin watan Ramadan.

 

Ya kara da cewa, “Muddin ni ne gwamnan jihar Borno, za a ci gaba da rabon kayayyakin jin kai. Duk da haka, ina so in jaddada cewa yayin da ake ci gaba da rabon kayan abinci, za mu ci gaba da bada tallafi harkar kasuwanci da noma”.

 

Ya bukaci al’ummar jihar da su himmatu wajen aikin noma don bunkasa samar da abinci, tare da ba da tabbacin samar da karin ababen more rayuwa da suka hada da shiga motocin bas kyauta, da kayan aikin gona da tallafin kudi don farfado da tattalin arzikin jihar.

 

Daga Dauda Iliya

 

 

Labarai

Labarai8 hours ago

Amurka Ta Dakatar Da Kudurin Kai Jirgin Bama-Bamai Zuwa Isra’ila

Amurka ta sanar da batun dakatar da shirin ta na kai jirgi dauke da bamabamai zuwa Israila a cikin makon...

Labarai9 hours ago

NAHCON Ta Jinjinawa Hukumar Alhazai Ta Jihar Jigawa Bisa Shirye-shiryen Hajjin Bana

Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa Alhaji Ahmed Umar Labbo ya karbi tawagar gani da ido...

Kasuwanci1 day ago

CBN Ya Bai Wa Masu POS Wa’adin Yin Rajista Da Gwamnati

Babban Bankin Najeriya CBN ya bayar da wa’adin ranar 7 ga watan  Yulin 2024 ga masu POS su kammala rajista...

Fasaha1 day ago

Kusan Malaman Makaranta Dubu 2 Ke Samun Horo a Barno

  Gwamnatin jihar Borno ta fara aikin horas da malamai 1,949 a matakin farko da aka gano cewa suna iya...

Fasaha1 day ago

Bankuna Za Su Fara Cirar 0.5% Daga Masu Tura Kudi Ta Intanet

  Babban Bankin Najeriya (CBN) ya umurci bankunan kasar su fara cirar kaso 0.5 cikin 100 na duk kuɗin da...

Labarai1 day ago

An kashe Falasɗinawa 34,800 tun fara yaƙi – Ma’aikatar lafiyar Hamas

Ma’aikatar lafiya ta Hamas a Gaza ta ce an kashe Falasdinawa 34,789 a yankin tun ranar 7 ga watan Oktoba,...

Ilimi4 days ago

Gwamnatin Jigawa Za Ta Samar Da Gidaje A Jami’ar Tarayya Da Ke Babura

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce za ta ci gaba da tallafawa harkokin koyo da koyarwa a Jami’ar Fasaha ta Gwamnatin...

Labarai5 days ago

An Samar Da Sabon Tsari Da Zai Inganta Harkar Noman Rogo A Najeriya

Shugaban kungiyar masu noman rogo ta Najeriya (NCGA), Mustapha Othman Bakano, ya kaddamar da wani tsari na samar da kasuwa...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Za Ta Samar Da Tarakta 300 Ga Manoma Daga Amurka

A kokarinta na ci gaba da habbaka harkokin noma, Gwamnatin Jihar Jigawa ta ƙulla wata yarjejeniyar haɗin gwiwa da wasu...

Labarai6 days ago

An kama masu zanga-zanga 17 a jami’ar Texas

An sake kama ƙarin mutanen da ke da alaƙa da zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasɗinawa inda a wannan karon...

Mafi Shahara