Labarai
An Kashe Jagoran ‘Yan Adawar Chadi Yaya Dillo
Hukumomin kasar Chadi sun tabbatar da mutuwar daya daga cikin shugaban ‘yan adawa Yaya Dillo bayan wani samame da jami’an tsaro suka kai ofishin jam’iyyarsa a jiya, wanda ya jefa mazauna birnin Ndjamena cikin fargaba da tashin hankali.
Mai gabatar da kara na gwamnatin Chadi Oumar Mahamat Kedelaye ya tabbatar da mutuwar shugaban ‘yan adawar a yau Alhamis, bayan artabun da akayi jiya.
Mutuwar Dillo na zuwa ne bayan da gwamnatin kasar ta zargi jam’iyyarsa da kai wani mummunan hari kan hukumar tsaron kasar, lamarin da ya musanta shi kai tsaye a jiya Laraba.
Harin da aka kai kan hukumar tsaron ya zo ne bayan da aka kama wani ‘dan jam’iyyarsa ta PSF tare da zargin sa da yunkurin kisan shugaban kotun kolin kasar.
A jiya Laraba ne aka ji karar harbe-harbe a kusa da hedikwatar jam’iyyarsa da ke N’Djamena babban birnin kasar.
Wannan na zuwa ne kwana guda da gwamnatin Chadi ta sanar cewa, za a gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 6 ga watan Mayu, inda shugaba Mahamat da Dillo za su fafata da juna.
Mahamat dai ya dare kan karagar mulki ne bayan mutuwar mahaifinsa Idriss Deby Itno wanda ya rasa ransa a yayin fafatawa da ‘yan tawaye a 2021, yayin da ya shafe kimanin shekaru 30 yana mulkar kasar kafin ajalinsa.
Har ya zuwa wannan lokaci mazauna babban birnin kasar na cikin fargaba dangane da abin da ka iya je ya komo, sakamakon arangamar ta jiya da kuma mutuwar shugaban ‘yan adawa
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
