Kamfanin sarrafa albarkatun mai na Najeriya, NNPCL ya ce ya gano haramtattun matatun mai 84 da haramtattun bututan mai 66 cikin makon da ya gabata a yankin Neja Delta.
Cikin wani saƙo da NNPCL ya wallafa a shafin X, ya ce “a makon da ya wuce, an gano haramtattun bututan mai 66 da haramtattun matatun mai 84 a yankin Neja Delta.”
Satar ɗanyan mai babbar matsala ce a Najeriya – ɗaya cikin mambobin ƙungiyar ƙasashe masu arzikin mai kuma ɗaya daga cikin ƙasashen nahiyar Afirka mafi samar da arzikin mai.
Najeriya dai tana asarar kusan gangar mai dubu ɗari biyu a duk rana saboda masu haramtattun matatun mai da kuma masu satar man.
Galibin mutane a yankin Neja Delta na rayuwa cikin talauci duk da cewa ƙasar ce mafi samar da man fetur a Afirka inda take samar da kusan ganga miliyan biyu duk rana