Labarai
NLC jihar Plateau ta bi sahun takwarorinta wajen zanga zangar tsadar rayuwa.

Shugaban kunguyar a Jihar Plateau Comrade Eugene Manji yace tsadar rayuwa da ake fuskanta a kasan Nan ya wuce tunanin kowane Dan kasan Nan.
Masu gangamin sunyi kwanba a shataletalen sakatariyar jihar inda suka bayyana irin damuwar da suke cikinta game da wannan tsaadar rayuwa da ta musu dabaibayi.
Shuganan kungiyar a jihar Plateau Comrade Eugene Manji yace cire tallafin Mai ba tare da wani kwakkwaran shiri ba, shi ne ummul’aba’isin fadawa cikin wannan masifar.
Hakama ya bayyana matukar damuwarsu game da canjin kudaden kasashen waje ya kasance.
Comrade Manjin duk da haka Kuma, gwamnati ta kasa cika alkawarinta na samarda motocin safa safa masu amfani da gas da gyaran matatun man fetur, da wutar lantarki da dai sauran matakan rage tsadar rayuwar ga ‘yan Nijeriya.
Ya bayyana matukar damuwarsa ganin cewa duk da tashin gwaron zabin kusan komai a kasan nan, amma albashin da ake biyan ma’aikata bai taka kara ya karya ba.
Sannan ya godewa ‘yan kwadago saboda amsa Kiran da sukayi suka yi fitowar farin dango duk irin matsin rayuwar da ake ciki, tare da shan alwashin kungiyar kwadago zata ci gaba da Kare hakkin ma’aikata da ‘yan Nijeriya ba tare da gajiyawa ba.
Farfesa Kiri Jaryam shi ne yayi magana a madadin kungiyar malaman jami’a ya bukaci dukkannin ‘yan Nijeriya da su hada kansu don a gudu tare a tsira tare.
Dr. Makuyai Godwin yayi magana a madadin kungiyar malaman kwalejojin kimiyya da fasaha da kuma Anthony Joro da ya wakilci kungiyar manyan ma’aikata sun bukaci gwamnati ta tabbatar da ‘yan Nijeriya sun sami saukin rayuwa.
Josiah/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
