Labarai
NLC Ta Yi Barazanar Shiga Zanga-zangar Kwanaki 2 A Fadin Najeriya
Kungiyar Kwadago ta Najeriya ta yi barazanar shiga zanga-zangar kasa ta kwanaki 2, idan har gwamnatin tarayya ta gaza aiwatar da yarjejeniyar da ta cimma da ma’aikata a karshen wa’adin kwanaki 14.
Da yake zantawa da manema labarai a Abuja, a karshen taron majalisar zartarwa ta kasa, shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya, Kwamared Joe Ajaero, ya ce za a fara zanga-zangar ne bayan cikar wa’adin kwanaki 14 da ta ba gwamnatin tarayya don magance yarjejeniyar da aka cimma. da Labour.
Kwamared Ajaero ya ce kungiyar Kwadago za ta fara zanga-zanga a fadin kasar a ranakun 27 da 28 ga watan Fabrairu.
Karamin Ministan Kwadago da Aiki, Dr Nkieruka Onyejeocha ya tabbatar wa kungiyar kwadagon cewa gwamnatin tarayya za ta cika yarjejeniyar da ta kulla da kungiyar kwadago cikin mako guda.
Dr Onyejeocha ya bayyana kudirin gwamnatin tarayya na tabbatar da jin dadin ma’aikatan Najeriya.
RN
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki