Connect with us

Ilimi

Yajin Aikin NASUU da SSANU Ya Gurgunta harkikin Karatu a Jami’o’in Nujeriya

Published

on

Yajin aikin da Kungiyar ma’aikatan Jami’o’i ta kasa da suka hada da NASUU da SSANU suka fara gudanar wa ya gurgunta harkokin karatu a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria.

Kungiyoyin ma’aikatan sun fara yajin aikin ne na kwanaki bakwai a matsayin na gargadi.

Wakilin Radio Najeriya ya bayyana cewa shugabannin Kungiyar sun rufe duk kofofin shiga Jami’ar inda dalibai da malamai na shiga harabar Jami’ar ce kawai ta hanyar taka sayyada.

Haka kuma kungiyoyin sun rufe duk wasu ayyuka a harabar dakunan kwanan dalibai da wuraren samar da ruwan sha da wutar lantarki da dakunan karatu,yayin da sauran ma’aikatan duk suka yi zaman su gida domin bin umurnin kungiyoyin.

Da yake zantawa da Radio Najeriya yayin wani tattaki da Yayan kungiyoyin suka gudanar daga ofishin Shugaban jami’ar zuwa babbar kofar shiga Jami’ar, shugaban gamayyar kungiyoyin, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar manyan ma’aikatan Jami’ar Ahmadu Bello, kwamared Mohammed Yunusa ya ce kungiyoyin sun hana gudanar da aiyukan Jami’ar ne tun ranar Litinin da aka fara yajin aikin kamar yadda uwar kungiyar ta kasa ta basu umurni.

Shugaban ya ce sun fara yajin aikin ne sakamakon rukon sakainar kashi da nuna bambanci da gwamnatin tarayya ke yi masu wajen biyan albashi da kuma gazawar gwamnati wajen cika alkawuran da ta yi a tsakanin su.

Kwamared Yunusa ya ce shugaban kasa ya bada umurnin a biya su amma wasu Jami’ai sun ki biya.

A cewar sa,Jami’an sun ki biyan su ne kasancewar basa daukar yayan kungiyoyin da muhimmanci wajen tafiyar da harkokin Jami’a,kasancewar kungiyar malaman Jami’o’i kawai suke ba muhimmanci.

Shugaban gamayyar kungiyoyin ya tunasar da gwamnati game da halin da harabar Jami’o’in za su kasance idan babu ruwa da wuta da kuma dakunan karatu da na bincike idan suka kasance a rufe.

Kwamared Mohammed Yunusa ya ce yajin aikin nasu ya yi nasara kasancewar yayan kungiyoyin biyu sun bi umurnin uwar kungiyar ta kasa.

Haliru Hamza

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Labarai13 hours ago

Gini Ya Fado Kan Mutane 11 A Kano

Wani gini ya fado kan ma’aikata suna tsaka da aikin gini a unguwar Kuntau da ke Karamar Hukumar Gwale a...

Ilimi15 hours ago

Gwamnatin Qatar Za Ta Tallafa Wa Marayu 1000 A Borno

Gwamnatin Kasar Qatar ta yi alkawarin tallafawa kimanin marayu dubu daya da rikicin Boko Haram ya rutsa da iyayensu. Jakadan...

Labarai3 days ago

Jihar Jigawa Za Ta Fara Allurar Rigakafi Da Bada Unifom Ga Alhazai

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce nan ba da dadewa ba za ta fara gudanar da allurar...

Ilimi3 days ago

Daliban Jihar Kebbi Da Ke Kasashen Waje Za Su Sami Tallafin Naira Miliyan 309

Gwamnatin jihar Kebbi, ta amince da kashe sama da Naira miliyan Dari Uku da Tara, domin biyan tallafin karatu na...

Kasuwanci3 days ago

Kwari Masu Lalata Amfanin Gona Sun Mamaye Gonakin Tumatur A Kano

Shugaban kungiyar manoma ta jihar Kano, AFAN, Abdullahi Maibreadi, ya bukaci gwamnati a dukkan matakai da su taimaka wa manoma...

Fasaha3 days ago

Shugaba Tinubu Ya Kaddamar Shirin Bada Bashin Kayyaki Ga ‘Yan Kasa

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ƙaddamar da kashin farko na tsarin karɓar bashin kaya ga ƴan ƙasar. Bayanin hakan na...

Labarai3 days ago

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Rufe Bankin UBA Kan Kin Biyan Haraji

Hukumar Tara Kudaden Haraji ta Jihar Kaduna (KADIRS) ta raufe rassan bankin UBA kan kin biyan harajin Naira miliyan 14....

Labarai4 days ago

Mutum Biyar Sun Mutu Cikin Kwale-Kwalen ƴan Ci-Rani

Mutum biyar har da yaro sun mutu yayin da suke ƙoƙarin tsallake hanyar ruwa da ta ratsa Ingila da safiyar...

Kasuwanci4 days ago

CBN Ya Sake Karya Farashin Dala Zuwa N1,101

Babban Bankin Nigeria CBN ya sake sanar da matakin karya farashin dala daga N1,251 zuwa N1,101. CBN ya bayyana haka...

Ilimi4 days ago

Ƴan Sanda Za Su Yi Bincike Kan Makarantar Leads British

Rundunar ƴan sanda a babban birnin tarayya Abuja ta ce ta aika tawagar jami’anta zuwa makarantar Leads British bayan bidiyon...

Mafi Shahara