Connect with us

Labarai

Gwamnatin Katsina Ta Sayo Motoci Masu Sulke Don Yaƙar ‘Yan Bindiga

Published

on

Gwamna Dikko Radda ya kaddamar da motoci masu sulke 10 domin yaki da ’yan bindiga da sauran masu tada kayar baya a Jihar Katsina.

Kamfanin Dillancin aLabarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito a yayin kaddamar da motocin ranar Litinin, Dikko Radda ya ce, za a raba motocin ne ga jami’an tsaron hadin gwiwa a jihar domin yakar ’yan bindiga da sauran masu aikata miyagun laifuka.

Ya bayyana cewa, za a kai motocin ne kananan hukumomi takwas da ’yan bindiga suka hana su sakat.

Kananan hukumomin sun hada da Safana da Batsari da Danmusa da Kankara.

Sai kuma Faskari, Sabuwa da Dandume da Jibia.

Ya ce, “Gwamnati ta kuduri aniyar kawar da ’yan bindiga da masu aikata miyagun laifuka a jihar Katsina.”

Radda ya kara da cewa, an samu nasarori da dama tun bayan fara aikin rundunar tsaro ta hadin gwiwa a jihar.

Ya kuma yabawa jami’an tsaro bisa kokarin da suke yi, inda ya bayar da tabbacin gwamnati za ta ci gaba da ba su tallafin da ya dace domin dawo da zaman lafiya a fadin jihar.

Gwamnan ya bukaci jama’ar jihar su rika taimaka wa jami’an tsaro da sahihan bayanai dangane da masu aikata miyagun laifuka a yankunansu a kan kari.

A nasa jawabin, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Dokta Nasiru Muazu-Danmusa, ya ce samar da motoci masu sulke ya nuna aniyar gwamnati na kare jama’a.

Ya ce, gwamnati za ta ci gaba da hada kai da jami’an tsaro domin kare al’umma da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

A nasa jawabin,  mataimakin kwamishinan ’yan sanda Ibrahim Saad, ya yaba wa gwamnati bisa samar da motocin, ya kuma yi alkawarin cewa za a raba su yadda ya kamata domin murkushe ’yan ta’adda, masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka

Labarai

Labarai12 hours ago

Gwamnatin Jigawa Za Ta Samar Da Tarakta 300 Ga Manoma Daga Amurka

A kokarinta na ci gaba da habbaka harkokin noma, Gwamnatin Jihar Jigawa ta ƙulla wata yarjejeniyar haɗin gwiwa da wasu...

Labarai12 hours ago

An kama masu zanga-zanga 17 a jami’ar Texas

An sake kama ƙarin mutanen da ke da alaƙa da zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasɗinawa inda a wannan karon...

Labarai1 day ago

An Samar Da Masauki Kusa Da Harami Ga Alhazan Jihar Jigawa

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa  ta samar da katafaren masauki  kusa da Masallacin Harami da ke birnin Makkah...

Labarai3 days ago

Kungiyar AFAN Ta Shirya Taron Bita Ga Manoman Jihar Jigawa

Hadaddiyar kungiyar manoma ta kasa reshen Jihar Jigawa da cibiyar binciken yanayin kasa dake Kaduna sun shirya wa manoma daga...

Fasaha4 days ago

An Bukaci Gwamnatin Sakkwato Ta Agaji Jami’ar Jihar

Kungiyar Malaman Jami’ar Jihar Sakkwato ASUU-SSU ta yi kira ga gwamnatin Jihar ta duba halin da kungiyar ke ciki da...

Kasuwanci4 days ago

Mun Aika Musu Takardun Gargadi Kafin Ginin Ya Rushe – KANUPDA

  Manajan Daraktan Hukumar Tsare-tsare da Ci gaban Birane ta Jihar Kano (KNUPDA), Architect Ibrahim Yakub Adamu ya yi gargadin...

Ilimi4 days ago

Zamu Zuba Jarin Dala Miliyan 600 a Nijeriya – Mr. Robert

Shugaba Kasa Bola Tinubu ya samu masu zuba jarin dala miliyan 600 daga kamfanin sufurin jiragen ruwa na kasar Denmark,...

Labarai6 days ago

Gini Ya Fado Kan Mutane 11 A Kano

Wani gini ya fado kan ma’aikata suna tsaka da aikin gini a unguwar Kuntau da ke Karamar Hukumar Gwale a...

Ilimi6 days ago

Gwamnatin Qatar Za Ta Tallafa Wa Marayu 1000 A Borno

Gwamnatin Kasar Qatar ta yi alkawarin tallafawa kimanin marayu dubu daya da rikicin Boko Haram ya rutsa da iyayensu. Jakadan...

Labarai1 week ago

Jihar Jigawa Za Ta Fara Allurar Rigakafi Da Bada Unifom Ga Alhazai

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce nan ba da dadewa ba za ta fara gudanar da allurar...

Mafi Shahara