Connect with us

Labarai

Waɗanda suka dakatar da Ganduje ba ƴan APC ba ne – Abdullahi Abbas

Published

on

Jam’iyyar APC a jihar Kano ta ce za ta ɗauki mataki kan ɓangaren da ya sanar da dakatar da tsohon gwamnan jihar kuma shugaban jam’iyyar APC ta ƙasa na riƙo, Abdullahi Umar Ganduje.

A ranar Litinin ne wani reshen mazaɓar Ganduje da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano ya sanar da dakatar da shugaban jam’iyyar ta kasa, daga bisani kuma shugaban jam’iyyar APC din a matakin ƙaramar hukumar Dawakin Tofa ya yi watsi da matakin.

Shugaban jam’iyyar APC a jihar, Abdullahi Abbas ya yi zargin cewa waɗanda suka dakatar da Ganduje makusanta ne ga wasu masu riƙe da muƙamai a gwamnatin jihar da NNPP ke mulki.

Ya shaida cewa sun duba jerin sunayen ƴan jam’iyyar na mazaɓar Ganduje, “mutum 27 ne kowace mazaɓa, mun duba a cikin su gaba ɗaya babu ko ɗaya da yake a cikin shugabanni.”

A cewarsa, jami’in da aka ce ya sanar da dakatar da Gandujen, Haladu Gwanjo, ya ce zai je kotu ya nemi haƙƙinsa saboda an zalunce shi.

Abdullahi Abbas ya bayyana cewa “wannan ba abin da ya haɗa shi da jam’iyyarmu, wannan tsari ne na gwamnatin jihar Kano da jam’iyyarsu ta kayan gwari suka shirya, ina tunanin wannan [ita ce] hanyar da za su ci mutuncin dakta Ganduje.”

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai1 week ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara