Labarai
Senegal Ta Kama Tan Guda Na Hodar Ibilis
Hukumar Kwastam ta Senegal ta ce ta kwato fiye da tan guda na hodar ibilis a kudu maso gabashin kasar, inda ta bayyana shi a matsayin kamu mafi girma da aka taba yi na jigilar hodar iblis a kan hanyar kasa a yammacin Afirka.
Hukumar ce an kama hodar ibilis mai nauyin kilogiram dubu daya da dari daya da talatin da bakwai da digo shidda a ranar Lahadin da ta gabata a garin Kidira, wacce ta kiyasta kudinsa zai kai sama da CFA biliyan 90, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 146.
Sanarwar ta ce, wannan shi ne kamu mafi girma na hodar iblis ta hanyar kasa da aka taba samu a Senegal.
Hukumar ta ce an boye hodar ne a cikin fakiti-fakiti kuma an sanya shi a cikin jakunkuna a wata mota mai daukar kayan sanyi da ta fito daga wata kasa mai makwabtaka da Senegal, wadda ba ta bayyana sunan kasar ba.
Kasar Senegal dai tana iyaka da kasashen Guinea da Gambia da Guinea Bissau da Mauritania da kuma Mali, kasashen da aka san su ne wuraren safarar magungunan da ake samarwa a Amurka ta Kudu akan hanyarsu ta zuwa Turai.
Yammaci da tsakiyar Afirka ya zama yankin da ake yawan amfani da shi, a cewar ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai yaki da miyagun kwayoyi da laifuffuka.
A watan Oktoban 2022, an kama kilogiram 300 na hodar iblis daga wata motar daukar kaya masu sanyi da ta taho daga Mali.
Haka kuma Rundunar sojin Senegal a watan Nuwamban bara, ta ce ta gano kusan tan uku na hodar iblis daga wani jirgin ruwa a gabar teku.
-
Labarai3 days ago
Kungiyar AFAN Ta Shirya Taron Bita Ga Manoman Jihar Jigawa
-
Labarai6 days ago
Gini Ya Fado Kan Mutane 11 A Kano
-
Fasaha3 days ago
An Bukaci Gwamnatin Sakkwato Ta Agaji Jami’ar Jihar
-
Labarai20 hours ago
An Samar Da Masauki Kusa Da Harami Ga Alhazan Jihar Jigawa
-
Kasuwanci3 days ago
Mun Aika Musu Takardun Gargadi Kafin Ginin Ya Rushe – KANUPDA
-
Ilimi6 days ago
Gwamnatin Qatar Za Ta Tallafa Wa Marayu 1000 A Borno
-
Labarai7 hours ago
Gwamnatin Jigawa Za Ta Samar Da Tarakta 300 Ga Manoma Daga Amurka
-
Ilimi3 days ago
Zamu Zuba Jarin Dala Miliyan 600 a Nijeriya – Mr. Robert