Labarai
‘Yan Sanda Sun Kama Tirelar Sata Makare Da Kaya A Bauchi
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi, ta cafke wani da ake zargin barawo ne da ya sace wata tirela dauke da tan 35 na man gyada da darajarsa ta kai kimanin Naira miliyan 30.
Rundunar ta samu rahoton sace tirelar da aka ajiye a yankin Maraban Jos a Jihar Kaduna a ranar 12 ga watan Afrilun 2024.
Kakakin rundunar, SP Ahmed Wakil, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, ya ce motar da aka sace mai lamba DAF CF 85, ta fito ne daga Umuahia a Jihar Abiya.
SP Wakil, ya ce bincike ya nuna cewa direban motar ya tsaya a Maraban Jos don yin wanka amma yana dawowa ya tarar an sace ta.
Kakakin ya ce rundunar ta samu damar kwato kaya masu yawa a cikin tirelar.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
