Connect with us

Labarai

An Nada Sarkin Dass A Matsayin Amirul Hajji Na Jihar Bauchi

Published

on

Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na jihar Bauchi ya amince da nadin Sarkin Dass Alhaji Usman Bilyaminu Othman, a matsayin Amirul Hajji na Jahar don gudanar da aikin Hajjin 2024 a kasa mai tsarki.

Wasikar nadin mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Barista Ibrahim Mohammed Kasim na nuni da cewa nadin nasa tare da wasu fitattun ‘yan jihar 13, an yi sa ne bisa jajircewar su da sadaukar da kai, da kiyaye dokokin  Allah Madaukakin Sarki.

Gwamna Bala Mohammed ya bayyana kwarin guiwar tawagar da aka nada, inda ya jjaddada cewa yana da yakimin za su yi aiki yadda yakamata.Ya nanata kudurin gwamnatin jihar na tallafawa alhazai da kuma tabbatar da jin dadin su a tsawon tafiyarsu.

Sauran membobin tawagar ta Amirul Hajj sun hada da mataimakin shugaban  majalisar jihar Honarabul  Jamilu Umar Dahiru a matsayin mataimakin Amirul Hajj,da mai shari’a Rabi Talatu Umar, Babbar Alkalin Jihar Bauchi, da
Khadi Umar Ahmed Liman, da Honarabul Yakubu Ibrahim Hamza, da kuma Honarabul.

Sauran sun hada da Alhaji Ibrahim Y.M Baba Hakimin Yelwan Duguri, da Galadiman Bauchi Surv. Ibrahim Saidu Jahun, da Alhaji Yayanuwa Zainabari
da  Sheikh Zubairu A. Madaki, da kuma Sheikh Salisu Sulaiman Ningi.

Har ila yau akwai Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi, da Malam Ahmad Inuwa Na’ibi, da kuma Muhammad Haruna Barde a matsayin sakataren tawagar.

Tawagar za ta yi aiki tare da hukumomin da abin ya shafa da suka hada da Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jiha, da Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) da kuma Gwamnatin Saudiyya, domin tabbatar da ganin an samu nasarar gudanar da aikin hajjin bana ga daukacin alhazan Jihar Bauchi.

Gwamnan ya bukaci tawagar da aka nada da ta bada himma wajen gudanar da ayyukanta, tare da tabbatar da bin gaskiya da  adalci.

 

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara