Connect with us

Labarai

Gwamnatin Bauchi Za Ta Biya Kashi 50 Na Cikon Kudin Aikin Hajji

Published

on

Gwamnan Jihar Bauchi Bala Muhammad ya amince da biyan kashi hamsin bisa dari na cikon kudaden aikin Hajjin 2024 ga Alhazan jihar.

Hakan ya biyo bayan sanarwar da Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta yi, na karin Nera Miliyan daya da dubu dari tara da goma sha takwas,  kan  Nera Miliyan hudu da dubu dari shida da suka biya a baya.

A don haka ne gwamnatin jihar Bauchi karkashin jagorancin Gwamna Bala Muhammad ta kudiri aniyar bada tallafi ga Alhazan jihar, inda za a biya wa kowani maniyyaci Nera dubu dari tara da hamsin da tara.

Gwamnan ya amince da a biya Nera Miliyan dubu biyu da dari daya da casa’in da shidda domin tallafawa maniyyatan jihar su dubu biyu da dari biyu da casa’in.

Safiyah Abdulkadir

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Labarai19 hours ago

Majalisar Dattijan Na So A Bai Wa Kananan Hukumomi Yancin Kai

Majalisar Dattijan Najeriya ta nemi Shugaba Tinubu ya shige gaba domin nema wa kananan hukumomi ‘yanci a wajen jihohi, wanda...

Labarai20 hours ago

‘Yan Ƙwadago Sun Yi Watsi Da N48,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

  Ƙungiyar Ƙwadago NLC ta yi fatali da tayin naira 48,000 da Gwamnatin Tarayya ta gabatar a matsayin mafi ƙarancin...

Labarai21 hours ago

Tinubu Zai Ciyo Bashin $500m Don Sayen Mitocin Lantarki

  Majalisar Dattawa ta sahale wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ciyo bashin Dala miliyan 500 da nufin samar da mitocin...

Ilimi22 hours ago

Za A Fara Daukar Masu Sakamakon Jarabawar NECO A Jami’o’in Birtaniya

  Jami’o’in kasar Birtaniya na shirin fara daukar daliban Najeriya masu shaidar jarabawar kammala sakandare ta NECO. Shugaban hukumar shirya...

Labarai2 days ago

Jirgin Farko Na Alhazan Najeriya Ya Tashi Zuwa Kasa Mai Tsarki

A yau Laraba 15 ga watan Mayun 2024 ne jirgin Najeriya na farko ya tashi da Alhazan Jihar Kebbi 423...

Labarai2 days ago

Najeriya Ta Kaddamar da Shafin Intanet Don Samun Bayanai Game da Ma’adinai

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shafin intanet ranar Talata wanda zai bai wa masu zuba jari damar samun cikakkun bayanai...

Labarai3 days ago

Tsohon Lauyan Trump Ya Ce Ubangidansa Ya Ba ‘Yar Fina-finan Batsa Toshiyar Baki

Tsohon babban lauyan Donald Trump, Michael Cohen, ya aikata abinda masu gabatar da kara su ka yi ta fatan ya...

Labarai3 days ago

Kotu Ta Yankewa Wani Mutum Hukuncin Zaman Gidan Yari Na Watanni 2 Bisa Satar Doya

Kotun Majistare da ke Gwagwalada a babban birnin tarayya Abuja, ta yanke wa wani mutum mai suna Isah Sani hukuncin...

Labarai3 days ago

Jamhuriyar Benin Ta Haramta Fitar Da Masara Zuwa Nijar

Jamhuriyar Benin ta hana fitar da masara zuwa ƙasashen waje a daidai lokacin da farashin hatsi ya yi tashin gwauron...

Labarai3 days ago

Gwamnatin Kano Ta Nada Ibrahim Garba Shugaban Tawagar ‘Yan Jarida A Hajjin Bana

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da nadin Ibrahim Garba Shuaibu a matsayin shugaban tawagar ‘yan jaridu a aikin Hajjin 2024....

Mafi Shahara