Connect with us

Labarai

Saqafatu Movement Foundation Ta Raba Kayan Sallah Ga Marayu.

Published

on

 

Kungiyar Saqafatu Movement Foundation ta raba kayayyakin Sallah ga marayu na dubban naira domin samun falalar wannan wata mai albarka na Ramadan.

Shugabar kungiyar, Malama Asiya Ado Yakasai ta sanarda hakan yayin taron rabon kayayyakin da ya gudana a harabar Masallacin Saqafa dake Barnawa Kaduna.

Ta ce, shekaru 10 kenan da kungiyar ta shafe wajen hidimar baiwa marayu kayan Sallah a irin wannan lokacin na azumin watan Ramadan domin samun falalarsa.

Malama Asiya Ado Yakasai ta nemi gwamnatin da masu ruwa da tsaki su taimaka wa marayu da mabukata musamman a wannan lokaci na matsin tattalin arzikin Kasan nan.

Da take tsokaci, Uwar kungiyar Saqafatu Movement Foundation, Malama Hafsat Yahaya Misau, ta ce, kungiyar tana baiwa marayu 160 kayan Sallah kowace shekara, inda a bana ta baiwa marayu 90 kadai, sakamakon wahalar tsadar rayuwa da ake fama da shi a yanzu.

Ta yi kira ga gwamnati da mawadata su tallafawa kungiyar wajen habaka ayyukanta na alkhairi domin samun tsira a gobe kiyama.

Da yake jawabi a wajen taron, Hakimin Barnawa, Alhaji Kabiru Zubair ya yabawa aikin alkhairin da kungiyar ke gudanarwa duk shekara na taimakawa Marayu.

Ya tunatarda al’uma akan falalar taimakawa Marayu tareda addu’ar Allah Ya sanyawa kungiyar lada a mizani.

Daya daga cikin marayun da suka samu tallafin kayan Sallah Zainab Hussaini ta yi addu’ar Allah Ya cigaba da tallawa kungiyar akan irin hidimar da suke yi ma Marayu.

A wurin taron, an rabawa marayu maza da mata 90 kayan Sallah da suka kunshi atamfofi da shadda da yadi.

Khadija Kubau

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara