Labarai
‘Yan Fashin Tekun Somalia Sun Sako Jirgin Bangladesh Bayan Karbar Kudin Fansa
‘Yan fashin tekun Somalia sun sako wani jirgin ruwan dakon kaya mai tutar Bangladesh tare da ma’aikatansa 23 a yau lahadi, bayan da masu jirgin suka biya kudin fansa.
Jirgin ruwan MV Abdullah wanda ke jigilar kusan tan dubu hamsin da biyar na kwal daga kasar Mozambique zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa, wasu gungun ‘yan fashin teku da dama ne suka shiga da shi a nisan kilomita 1,000 daga gabar tekun Somalia wata guda da ya gabata.
“Mun cimma yarjejeniya da ‘yan fashin,” in ji Mizanul Islam, na kamfanin SR Shipping, mallakin kungiyar KSRM ta Bangladesh.
A cikin watan Maris, dakarun sa kai na India sun kutsa cikin jirgin ruwan Malta MV Ruen, wanda ‘yan fashin tekun Somalia ke rike da shi tun watan Disambar 2023. Wannan dai shi ne nasara na farko da aka samu na fashin teku a gabar tekun Somalia tun shekara ta 2017.
Ma’aikatan jirgin su 17, ‘yan Bama mutum 9, da ‘yan Bulgaria 7 da kuma dan Angola guda, an ceto su ba tare da wani rauni ba, sannan an kai ‘yan fashin 35 zuwa Bombay na kasar India domin gurfanar da su a gaban Kuliya.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
