Ilimi
Jihar Bauchi Za Ta Yi Aiki Da Hukumar Kula Da Almajirai Ta Kasa
Gwamnatin jihar Bauchi za ta hada gwiwa da Hukumar Almajiri da Yara da basa zuwa Makaranta don daukar nauyin karatun yara marasa galihu.
Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi ya bayyana kwarin gwiwar sabbin shugabannin Hukumar Almajirai da Ilimin Yara da ba su zuwa Makarantu na kasa wajen biyan bukatun yaran da abin ya shafa a kasar nan.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya gana da Babban Sakataren Hukumar Dokta Muhammad Sani Idris wanda ya ziyarce shi a gidan gwamnati da ke Bauchi.
Gwamna Muhammad ya ce idan aka yi la’akari da tarihi da dimbin gogewar Sakataren Zartaswa, za a tunkari kalubalen Almajiri da yaran da ba sa zuwa makaranta.
A baya dai Sakataren zartaswar ya ziyarci Uwargidan Gwamnan Jihar Bauchi, Dakta Aisha Bala Muhammad wadda ta nemi goyon bayan hukumar wajen shigar da ilimin boko a cikin manhajar karatun almajirai karkashin aikinta na Pet project na gidauniyar AlMuhibba da kuma gidauniyar Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Dokta Aisha Muhammad ta ce da irin dimbin gogewar da shugaban Hukumar Almajiri da Ilimin Yara da ba su zuwa Makarantu ke da ita, ta yi fatan hadin gwiwar da ake so da za ta tsara makomar miliyoyin yara masu rauni a kasar nan.
Sakataren zartarwa ya bayyana jin dadinsa da tarbar da aka yi masa a yayin ziyarar tare da bayar da tabbacin bada hadin kai don cimma manufofin.
Alhassan Usman/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
