Connect with us

Fasaha

Sheikh Dahira Bauchi YA Sa Albarka Ga shirin Sa Ilimin Boko Ga Manhajar Makarantun Allo

Published

on

Fitaccen Malamin Addinin Musulunci a Bauchi Sheik Dahiru Usman Bauchi Ya Amince Da Hada Ilimin boko da Manhajin Almajiri.

 

Jagoran mabiya darikar Tijjaniya Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya ce yana goyon bayan shirin gwamnatin tarayya na sanya ilimin boko a cikin manhajar karatun makarantun Almajiri.

 

Ya bayyana haka ne a lokacin da Babban Sakataren Hukumar Almajiri da Ilimin Yara marasa Makaranta ta kasa NCAOOSCE Dr Muhammad Sani Idris ya ziyarce shi a Bauchi.

 

Sheikh Dahiru Bauchi ya ce kungiyar Tijjaniya ta dukufa wajen ganin ta aiwatar da duk wani tsari da zai inganta zamantakewa da tattalin arzikin kasar nan.

 

Tun da farko Sakataren zartarwa na NCAOOSCE ya shaida wa Shehin Malamin cewa ya je gidansa ne domin neman albarkar sa yayin da ya fara ziyarce ziyarce don sake fasalin karatun Almajirai tare da kwashe miliyoyin yaran da ba sa zuwa makaranta a kan tituna.

 

Ya kuma jaddada cewa hadakar za ta baiwa almajirai damar samun ilimi da fasaha don yin gogayya a duniya.

 

Dr Muhammad Sani Idris ya kuma ce shugaban kasa Bola Tinubu ya damu da matsalar almajirai da yaran da ba su zuwa makaranta kuma ba zai bar wata kafa da za ta bi don kawo karshen ta ba.

Alhassan Bauchi/Wababe

Labarai

Labarai21 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai23 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara