Labarai
Ana Gudanar da Zaɓen Shugaban Kasar Senegal
Yan ƙasar Senegal na kaɗa ƙuri’a ranar Lahadi a zaɓen shugaban ƙasar bayan shekaru uku ana tayar da jijiyoyin siyasa sakamakon tuhumar da aka yi wa jagoran ƴan hamayya Ousmane Sonko da kuma fargabar da aka yi cewa shugaban ƙasar zai tsawaita wa’adin mulkinsa.
Ƴan takara 19 ne za su fafata domin neman wanda zai maye gurbin Shugaba Macky Sall, wanda zai sauka daga mulki bayan ya kammala wa’adi biyu.
Mutum miliyan 7.3 ne suka yi rajista a zaɓen sai dai ana ganin fafatawar za ta fi zafi tsakanin ɗan takarar gamayyar jam’iyyu masu mulki firaiminista Amadou Ba da babban ɗan hamayya Bassirou Diomaye Faye.
Dukansu sun taɓa aiki a hukumar karɓar haraji ta ƙasar, sai dai yanzu kowannensu yana da manufofi da suka sha bamban. Ba, mai shekara 62, ya yi alƙawarin ci gaba da tsarin da shugaba mai ci yake kai, yayin da Faye, mai shekara 43 ya sha alwashin kawo gagarumin sauyi.
Kowannensu ya bugi ƙirji cewa zai lashe zaɓen a zagayen farko — sai dai akwai yiwuwar ta tafi zagaye na biyu, domin kuwa akwai ƴan takara 15 a zaɓen, ciki har da mace guda ɗaya.
Za a rufe rumfunan zaɓe ne da misalin ƙarfe shida na yamma a agogon Dakar kuma ana sa ran soma sanar da sakamakon zaɓen da tsakar dare.
Ɗaruruwan masu jami’ai daga Tarayyar Afirka da ECOWAS da kuma Tarayyar Turai ne za su sanya ido kan zaɓen.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
