Labarai
ECOWAS Za Ta Kashe Dala Miliyan 25 Don Yaki Da Ta’addanci A Najeriya Da Nijar
Kungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ta ware Dala miliyan 25 da zimmar yaƙi da ta’addanci a ƙasashen Najeriya, da Nijar, da Mali, da Burkina Faso.
Ecowas ta tsara kashe kuɗin ne a shekarar 2024, kamar yadda Kwamashinar Raya Al’umma ta ECOWAS Farfesa Fatou Sarr ta bayyana a hedikwatar ƙungiyar da ke Abuja yau Juma’a.
Farfesar ta ce an ware miliyan huɗu daga cikin kuɗin don ayyukan agaji musamman ga mutanen da bala’o’i suka shafa.
“Haka nan, ECOWAS ta ware dala miliyan ɗaya da zimmar daidaita rayuwar mutanen da ta’addanci ya shafa, kamar ‘yan gudun hijira da kuma waɗanda aka ji wa rauni,” inji ta.
Ta ƙara da cewa a 2023 kaɗai, ECOWAS ta ba da tallafin Dala miliyan goma sha biyu da dubu dari shida ga mutane sama da miliyan huɗu da ta’addanci ya shafa a yammacin Afirka.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
