Kasuwanci
Tinubu Yayi Sabbin Nade-Nade A Kasuwar Shinko Ta Kasa

Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Mista Mairiga Aliyu Katuka a matsayin shugaban Hukumar kula da kasuwannin shinko na kasa.
Wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya fitar ta ce shugaban ya kuma nada Mista Emomotimi Agama a matsayin babban Darakta hukumar.
Frana Chukwuogor kuma an nada shi a matsayin Babban Kwamishinan kula da harkokin Shari’a.
Sai kuma Mista Bola Ajomale a matsayin Babban Kwamishinan kula da Ayyuka. Ita kuma Mrs. Samiya Hassan Usman a matsayin kwamishinar kula da harkokin hukumar.
Mista Lekan Belo kuwa a matsayin kwamishinan zartarwa. Da kuma Kasimu Garba Kurfi a matsayin Kwamishina.
Sanarwar ta kara da cewa, shugaba Tinibu ya bayyana kwarin gwiwar cewa dukkan mambobin hukumar za su yi amfani da kwarewarsu wajen ci gaba da aikin hukumar na samar da ingantacciyar kasuwa mai inganci, da gaskiya, ta yadda masu zuba jari za su samu kwarin gwiwa tare da bayar da gudummawa sosai ga harkokin kasuwanci. ci gaban tattalin arzikin kasa.
Bello Wakili/Wababe
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
