Labarai
‘Yan Bindiga Sun Harbe Wani Basarake A Jihar Taraba
A safiyar Juma’a 19 ga watan Afrilun 2024, al’ummar masarautar Sansani da ke karamar hukumar Gassol a jihar Taraba suka wayi gari da mummunan labarin kisan da wasu ‘yan bindiga suka yi wa Basarake Abdulmutallib Nuhu.
Wannan lamari ya faru ne ‘yan sa’o’i kadan kafin a fara bikin kamun kifi na Nwonyo, wanda ya shafe shekaru 14 ba a yi ba, sai a wannan lokaci da gwamnatin Gwamna Agbu Kefas ta sake farfado da shi.
An shirya gudanar da bikin ne a karamar hukumar Ibi ta jihar, kusa da kogin Benue a kudancin jihar ta Taraba.
Sansani yana da nisan kilomita kaɗan daga karamar hukumar Ibi, wurin da aka keɓe don bikin Kamun Kifin na Nwonyo.
A cewar Danmasanin Sansani, Salihu Sansani, kuma yayan marigayin, ‘yan bindigar sun isa garin Sansani ne da misalin karfe 9 na daren ranar Alhamis, inda suka doshi fadar kai tsaye suka kashe sarkin.
Ya shaida wa manema labarai cewa maharan sun zo ne a kan babura, inda suka harbe dan uwansa, sannan suka arce da wayoyinsa guda biyu.
“A yayin da suke barin kauyen, sun ci karo da wani matashi a kan babur, inda suka harbe shi a kafa.” in ji Danmasani.
Sai dai wani babban jami’in ‘yan sanda da ke aiki a yankin Sansani ya shaida wa wakilinmu cewa tuni rundunarsa ta fara bibiyar wadanda suka kashe babban basarake.
A lokacin hada wannan rahoto, Mukaddashin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, ASP James Lashen, ya bayyanawa manema labarai ta wayar tarho cewa yana kan hanyarsa ta zuwa ofishin don sanin halin da ake ciki game da lamarin.
Sani Sulaiman
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai21 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai23 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
