Labarai
Fitaccen jarumin Nollywood Amaechi Muonagor ya mutu

![]()
Fitaccen jarumin Nollywood, Amaechi Muonagor ya mutu yana da shekara 62 a duniya, kamar yadda wani ɗan’uwansa ya shaida wa manema labarai.
Ya mutu ne ranar Lahadi bayan ya yi fama da ciwon ƙoda da ya sa ake yi masa wankin ƙodar, in ji rahotanni daga kafafen yaɗa labarai.
Ɗan’uwan jarumin Tony Muonagor da aka fi sani da Tony Oneweek, ya tabbatar da mutuwar ɗanfim ɗin
Mutuwar tasa na zuwa ne ƴan kwanaki bayan da ya nemi tallafin kuɗi domin yi masa dashen ƙoda a Indiya.
Da yawa cikin masu son fina-finansa sun yi ta jimamin rasuwarsa a shafukan sada zumunta.
Muonagor ya yi fina-finai da dama ciki har da shahararren fim ɗin nan na Aki da Paw Paw, ɗaya daga cikin fitattun fina-finan da ya taka rawa a matsayin mahaifin yaran.
Mutuwarsa ta zo ƴan makonni bayan da Najeriya ta yi rashin wani jarumin Nollywood John Okafor da aka fi sani da Mista Ibu wanda shi ma ya buƙaci tallafin kuɗi domin neman magani.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
