Connect with us

Ilimi

Daliban Makarantar Kuriga Sun Shaki Iskar ‘Yanci – Uba Sani

Published

on

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da sakin yara ‘yan makaranta  dari biyu da tamanin da bakwai 287 da aka yi garkuwa da su daga Kuriga da ke karamar hukumar Chikun ta jihar

 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun gwamnan jihar Uba Sani.

 

Sanarwar ta ce “Ina so in sanar da cewa an sako yaranmu na makarantar Kuriga, muna godiya ta musamman ga mai girma shugaban mu, Bola Ahmed Tinubu, bisa ba da fifiko ga tsaro da tsaron ‘yan Nijeriya, musamman kokarin da ya yi na ganin an sako ‘ya’yan makarantar Kuriga da aka sace ba tare da wani lamuni ba”.

Gwamnan ya kuma yaba da jajircewar hafsoshin sojojin Najeriya na ganin an samu nasarar sako yaran.

 

Muna kuma gode wa daukacin ‘yan Najeriya bisa addu’in da suka yi na ganin  Allah Ya dawo da yaran cikin koshin lafiya, lallai wannan ranar farin ciki ce. Muna godiya ga Allah Madaukakin Sarki.”

 

Idan dai za a iya tunawa, a ranar 7 ga watan Maris, 2024, ‘yan bindiga suka sace ‘yan makarantar firamare  da na  Sakandaren Gwamnati da ke Kuriga, inda suka kai su dajin.

 

Masu garkuwa da mutanen sun bukaci a bada kudin fansa na Nera milyan dubu daya, yayin da suka ba da wa’adin ranar 27 ga Maris, 2024, don biyan kudin.

 

Aminu Dalhatu

Labarai

Labarai16 hours ago

Gini Ya Fado Kan Mutane 11 A Kano

Wani gini ya fado kan ma’aikata suna tsaka da aikin gini a unguwar Kuntau da ke Karamar Hukumar Gwale a...

Ilimi18 hours ago

Gwamnatin Qatar Za Ta Tallafa Wa Marayu 1000 A Borno

Gwamnatin Kasar Qatar ta yi alkawarin tallafawa kimanin marayu dubu daya da rikicin Boko Haram ya rutsa da iyayensu. Jakadan...

Labarai3 days ago

Jihar Jigawa Za Ta Fara Allurar Rigakafi Da Bada Unifom Ga Alhazai

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce nan ba da dadewa ba za ta fara gudanar da allurar...

Ilimi3 days ago

Daliban Jihar Kebbi Da Ke Kasashen Waje Za Su Sami Tallafin Naira Miliyan 309

Gwamnatin jihar Kebbi, ta amince da kashe sama da Naira miliyan Dari Uku da Tara, domin biyan tallafin karatu na...

Kasuwanci3 days ago

Kwari Masu Lalata Amfanin Gona Sun Mamaye Gonakin Tumatur A Kano

Shugaban kungiyar manoma ta jihar Kano, AFAN, Abdullahi Maibreadi, ya bukaci gwamnati a dukkan matakai da su taimaka wa manoma...

Fasaha3 days ago

Shugaba Tinubu Ya Kaddamar Shirin Bada Bashin Kayyaki Ga ‘Yan Kasa

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ƙaddamar da kashin farko na tsarin karɓar bashin kaya ga ƴan ƙasar. Bayanin hakan na...

Labarai3 days ago

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Rufe Bankin UBA Kan Kin Biyan Haraji

Hukumar Tara Kudaden Haraji ta Jihar Kaduna (KADIRS) ta raufe rassan bankin UBA kan kin biyan harajin Naira miliyan 14....

Labarai4 days ago

Mutum Biyar Sun Mutu Cikin Kwale-Kwalen ƴan Ci-Rani

Mutum biyar har da yaro sun mutu yayin da suke ƙoƙarin tsallake hanyar ruwa da ta ratsa Ingila da safiyar...

Kasuwanci4 days ago

CBN Ya Sake Karya Farashin Dala Zuwa N1,101

Babban Bankin Nigeria CBN ya sake sanar da matakin karya farashin dala daga N1,251 zuwa N1,101. CBN ya bayyana haka...

Ilimi4 days ago

Ƴan Sanda Za Su Yi Bincike Kan Makarantar Leads British

Rundunar ƴan sanda a babban birnin tarayya Abuja ta ce ta aika tawagar jami’anta zuwa makarantar Leads British bayan bidiyon...

Mafi Shahara