Ilimi
An Bukaci Masu Hannu Da Shuni Su Rika Taimakawa Marasa Galihu a Watan Ramadan
An bukaci masu hannu da shuni da su taimaka wa marasa karfi dake cikin al’umma domin su gudanar da azumin watan Ramadan cikin sauki.
Marafan Yamman Zazzau, Alhaji Adamu Ubaidullah ya yi kiran lokacin da ya zanta da wakilin Radio Najeriya a zaria.
Ya bayyana cewa idan aka yi la’akari da matsin tattalin arzikin kasa ke fuskanta ya zama wajibi al’umma su rungumi dabi’an taimaka wa junan su, musamman a wannan wata na azumin watan Ramadan.
Marafan Yamman na Zazzau ya ce akwai dimbin laba ga duk mutumin da ya ciyar da wani a wannan lokaci, musamman ganin yadda kayan masarufi ya yi tsada ta yadda mutane da dama basa iya ciyar da iyalan su.
Alhaji Adamu Ubaidullahi ya kuma shawarci jama’a da su yi amfani da wannan watan mai albarka wajen yin addu’o’in Allah ya kawo wa kasar nan mafita,musamman ta fuskar rashin tsaro da kuma magance talauci.
Ya kuma bukaci gwamnatoci a dukkan matakai da su maida hankali wajen taimakawa kananan manoma domin su iya gudanar da mona idan damina ta fadi.
Ubaidullahi ya bayyana cewa dole sai gwamnati ta tallafawa manoma kasancewar kayan aikin noma ya yi matukar tsada ga kuma rashin ratso dake neman hana yin noman.
Ya kara da cewa kamata ya yi gwamnati ta sa hannun sarakunan gargajiya yayin taimaka wa manoman kasancewar sune suka san manoman gaskiya ba manoman biro ba.
Marafan Yamman Zazzau ya yaba wa maimartaba sarkin zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli bisa jajircewar da ya yi na samar da sauye-sauye domin ciyar da masarautar Zazzau gaba.
A don haka sai ya bukaci al’ummar masarautar Zazzau da su gaba da baiwa maimarta sarkin na Zazzau goyon baya da hadin kai domin ya sami karin karfin gwiwar samar da alhairai ga masarautar.
INT/HALIRU HAMZA
-
Labarai3 days ago
Jihar Jigawa Za Ta Fara Allurar Rigakafi Da Bada Unifom Ga Alhazai
-
Kasuwanci4 days ago
CBN Ya Sake Karya Farashin Dala Zuwa N1,101
-
Fasaha3 days ago
Shugaba Tinubu Ya Kaddamar Shirin Bada Bashin Kayyaki Ga ‘Yan Kasa
-
Labarai18 hours ago
Gini Ya Fado Kan Mutane 11 A Kano
-
Labarai5 days ago
An Kwashe Mutane Da Dama Bayan Mummunar Ambaliyar A China
-
Fasaha5 days ago
Mutane 3 Sun Mutu a Salga a Kano
-
Labarai5 days ago
Shugaban Hukumar Leken Asirin Isra’ila Ya Yi Murabus
-
Kasuwanci4 days ago
Gwamnatin Jihar Kwara Ta Dakatar Da Yanka Nama A Mahauta Na Kwanaki 3