Labarai
Mataimakin Shugaban Tanzaniya Na Barazanar Yin Murabus Saboda Matsalar Karancin Ruwa
Mataimakin shugaban ƙasar Tanzaniya, Phillip Mpango ya yi barazanar sauka daga muƙaminsa saboda matsalar ƙarancin ruwan sha da aka daɗe ana fama da ita a lardin Mwanga da ke arewacin ƙasar.
Mista Mpango ya zargi ƴan kwangilar da ke kula da muhimmin aikin samar da ruwan sha a yankin na ɗaukan lokaci kafin kammala shi.
Shirin na sama da dala dubu 100 an soma shi ne kusan shekara 20 da ta gabata, a cewar Mista Mpango.
“Idan har aikin nan ba zai samar da ruwa ba ga mutanen yankin nan da watan Yuni, zan sauka.” Inji Mista Mpango.
“Ba zan sake zuwa nan na faɗa wa jama’a su ƙara hakuri ba, ruwa shi ne rayuwa,” ya ce.
A cewar jami’an gwamnati da suka yi wa Mista Mpango rakiya zuwa Mwanga a ranar Alhamis, an yi kashi 90 cikin 100 na aikin samar da ruwan.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai21 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai23 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
