Connect with us

Labarai

Dokar Auren Jinsi: Majalisar Ghana Ta Fusata Da Matakin Nana Akufo Addo

Published

on

Kakakin Majalisar Ghana ya ki amincewa da sahale nadin wasu sabbin ministoci bisa kafa hujja da cewa har sai shugaban kasar Nana Akufo-Addo ya sanya hannu a dokar haramta auren jinsi da Majalisar ta kada kuri’ar amincewa da ita a watan jiya, amma har zuwa yanzu shugaban ya gaza sanya hannu.

Ana dai ganin shugaba Nana Akufo-Addo na jan kafa wajen rattaba hannu kan kudirin don mayar da shi doka ne sakamakon kakkausar sukar da kudirin ke fuskanta daga kungiyoyin kare hakkin dan adam musamman daga kasashen Turai.

 

Kafin wannan mataki na Majalisar dai, shugaba Addo ya ce yana jiran hukuncin kotun kolin kasar gabanin rattaba hannu kan dokar, bayan da masu fafutukar tabbatar da auren na jinsi suka daukaka kara kan matakin.

 

Wasu alkaluma da aka tattara na nuna cewa galibin al’ummar Ghana na goyon bayan haramta auren na jinsi da kuma tanadin hukunci mai tsauri kan wadanda aka samu da aikatawa ko kuma da goyon baya koma tallata shi.

 

Sai dai wasu bayanai na cewa, shugaba Akufo-Addo ya samu gargadi ne daga kasashen duniya da hukumomin bayar da lamuni da ke neman lallai kar ya sanya hannu a kudirin don mayar da shi dokar.

Ghana dai ba ita ce kasar farko da ke fuskantar matsala wajen aiwatar da wannan doka ta haramta auren jinsi ba, domin kuwa makamancin lamarin da ke faruwa a Kenya kenan, inda har zuwa yanzu kungiyoyin addinai ke ci gaba da gangami don kalubalantar mahukunta.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Labarai4 hours ago

Amurka Ta Dakatar Da Kudurin Kai Jirgin Bama-Bamai Zuwa Isra’ila

Amurka ta sanar da batun dakatar da shirin ta na kai jirgi dauke da bamabamai zuwa Israila a cikin makon...

Labarai4 hours ago

NAHCON Ta Jinjinawa Hukumar Alhazai Ta Jihar Jigawa Bisa Shirye-shiryen Hajjin Bana

Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa Alhaji Ahmed Umar Labbo ya karbi tawagar gani da ido...

Kasuwanci1 day ago

CBN Ya Bai Wa Masu POS Wa’adin Yin Rajista Da Gwamnati

Babban Bankin Najeriya CBN ya bayar da wa’adin ranar 7 ga watan  Yulin 2024 ga masu POS su kammala rajista...

Fasaha1 day ago

Kusan Malaman Makaranta Dubu 2 Ke Samun Horo a Barno

  Gwamnatin jihar Borno ta fara aikin horas da malamai 1,949 a matakin farko da aka gano cewa suna iya...

Fasaha1 day ago

Bankuna Za Su Fara Cirar 0.5% Daga Masu Tura Kudi Ta Intanet

  Babban Bankin Najeriya (CBN) ya umurci bankunan kasar su fara cirar kaso 0.5 cikin 100 na duk kuɗin da...

Labarai1 day ago

An kashe Falasɗinawa 34,800 tun fara yaƙi – Ma’aikatar lafiyar Hamas

Ma’aikatar lafiya ta Hamas a Gaza ta ce an kashe Falasdinawa 34,789 a yankin tun ranar 7 ga watan Oktoba,...

Ilimi4 days ago

Gwamnatin Jigawa Za Ta Samar Da Gidaje A Jami’ar Tarayya Da Ke Babura

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce za ta ci gaba da tallafawa harkokin koyo da koyarwa a Jami’ar Fasaha ta Gwamnatin...

Labarai5 days ago

An Samar Da Sabon Tsari Da Zai Inganta Harkar Noman Rogo A Najeriya

Shugaban kungiyar masu noman rogo ta Najeriya (NCGA), Mustapha Othman Bakano, ya kaddamar da wani tsari na samar da kasuwa...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Za Ta Samar Da Tarakta 300 Ga Manoma Daga Amurka

A kokarinta na ci gaba da habbaka harkokin noma, Gwamnatin Jihar Jigawa ta ƙulla wata yarjejeniyar haɗin gwiwa da wasu...

Labarai6 days ago

An kama masu zanga-zanga 17 a jami’ar Texas

An sake kama ƙarin mutanen da ke da alaƙa da zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasɗinawa inda a wannan karon...

Mafi Shahara