Connect with us

Ilimi

Daliban Jami’ar Nasarawa 3 Sun Mutu A Tirmitsitsin Rabon Tallafi

Published

on

Daliban Jami’ar Jihar Nasarawa 3 ne ake fargabar sun mutu  sakamakon turmutsitsin da ya faru a lokacin rabon tallafin shinkafa da gwamnatin jihar ta bada a yau Juma’a a garin Keffi.

Lamarin ya faru ne a dandalin taro na makarantar inda aka ajiye buhunan shinkafa ana jiran isowar gwamna Abdullahi Sule domin fara rabon kayayyakin.

A cewar wani dalibin da lamarin ya faru a gaban idonsa, Moses Ajah, ya ce gungun daliban da ke dakon shiga dandalin sun ci karfin jami’an tsaro tare kutsawa dandalin taron.

Ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici matuka.

Ya ce wasu dalibai  sun kwashi buhunan shinkafan suka gudu da su  duk da cewa Gwamnan bai kai ga  iiowa wurin ba domin kaddamar da rabon.

Ya  zuwa lokacin hada wannan rahoto, an ga jami’an ‘yan sanda suna bin daliban dakunan kwanansu don kwato buhunan shinkafar da suka yi awan gaba da su.

Da aka tuntubi jami’in yada labarai da kula da jami’ar, Mista Abraham Ekpo, ya ce yana sane da lamarin amma har yanzu bai samu cikakken bayani a kai ba.

Aliyu Muraki

 

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara