Labarai
Zaben Senegal : Jami’yyar Adawa Ce Ke Kan Gaba
Sakamakon farko na zaben shugaban kasar Senegal na nuna dan takarar jam’iyyar adawa Bassirou Diomaye Faye ne ke kan gaba, lamarinn da ya sanya magoya bayansa fita kan tituna don fara nuna murnar nasara a zaben, ko da yake babban abokin hamayyarsa na jam’iyyar da ke mulki ya ce sai an gudanar da zaben zagaye na biyu ne za a iya tantance wanda yayi nasara.
Tuni dai akalla ‘yan takara 5 daga ciki 19 da ke fafatawa a zaben, suka fidda sanarwar taya Faye murna, duk da ya ke tsohon firai ministan kasar Amadou Ba da ke takara a jam’iyar da ke mulki ya ce ya yi wuri mutane su fara murnar sakamakon farko na zaben.
Miliyoyin mutane ne dai suka kada kuri’ar zaben shugaban Senegal na biyar a tarihi, don zabo wanda zai maye gurbin Shugaba Macky Sall da gwamnatinsa ta sha suka kan rashin samar da tsarin saukaka matsin tattalin arziki.
A cewar kafar talabijin din kasar, kashi 71 na yawan masu kada kuri’a miliyan 7 da dubu dari 3 ne suka yi zabe a kasar da ke da akalla yawan mutane miliyan 18.
Sakamakon farko na zaben da aka bayyana a gidan talabijin din kasar ya nuna cewa Faye ne ke kan gaba, lamarin da ya sa magoya bayansa fara gudanar da bukukuwa a titunan Dakar babban birnin kasar.
Kawo yanzu dai ba a tan-tance yawan adadin sakamakon rumfunan zabe nawa ne aka kirga ba, daga cikin dubu 15 da dari 633.
A gobe Talata ce ake sa ran fidda sakamakon zaben da dan takara ke bukatar lashe kashi 50 na yawan kuri’un da aka kada kafin yin nasara, ko kuma a je zagaye na biyu.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
