Labarai
Kotu Ta Bayyana Shuruddan Bada Belin Murja Kunya
Babbar kotun jihar Kano ta amince da bada belin shahararriyar yar Tiktok din nan mai suna Murja Ibrahim Kunya.
A hukuncin da ya yanke a ranar Litinin, Mai shari’a Nasiru Saminu ya amince da bada belin Murja Kunya a kan kudi Nera Milyan Dari Biyar tare da kawo mutane biyu da za su tsaya mata .
Daya daga cikin wanda zai tsaya mata, dole ya zama makusancin Murja Kunya na biyu kuma wajibi ne ya kasance yana da kadara a cikin ikon kotun.
Bayan haka, kotun ta umurci hukumar kula da asibitocin jihar Kano da kuma asibitin masu tabin hankali da su tabbatar da sallamar Murja bayan sun cika sharuddan belin.
Kotun ta dage zamanta zuwa ranar 16 ga watan Mayu, 2024 domin sauraren karar.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai21 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai23 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
