Ilimi
Girmama Hukuncin Kotu Muhimmin Jigo Ga Dimokuradiyya – Farfesa Fagge
An shawarci shugabanni da aka zaba da su girmama hukuncin kotu domin tabbatar da dimokuradiyya a ƙasar.
Wani malami a Jami’ar Bayero ta Kano, Farfesa Kamilu Fagge, ya bayar da wannan shawara a Kaduna, yana nuna damuwarsa kan zargin karya dokokin kotu a harkokin siyasa.
Ya bayyana damuwarsa kan matakin da Gwamna Ademola Adeleke na Jihar Osun ya dauka na gudanar da zaɓen kananan hukumomi duk da umarnin kotu da ke hana hakan.
Farfesa Fagge ya gargaɗi shugabanni da aka zaɓa cewa rashin mutunta hukuncin kotu, duk da rantsuwar da suka yi na kare kundin tsarin mulkin ƙasa da bin doka, na iya zama barazana ga dimokuradiyya.
SULEIMAN KAURA
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai21 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai24 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
