Ilimi
Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Dauki Nauyin Dalibai 80 Da Ke Manyan Makarantu
Karamar hukumar Birnin Kudu dake Jihar Jigawa ta ce za ta dauki nauyin dalibai ‘yan asalin yankin su 80 da ke kwalejin Ilmi ta tarayya ta Jama’are a Jihar Bauchi, da kwalejin fasaha ta Dutse da kuma kwalejin fasahar sadarwa ta Kazaure.
Shugaban Karamar Hukumar, Dr. Muhammed Uba Builder ya bayyana haka ga manema labarai a Birnin Kudu.
Dr Muhammad Uba, yayi bayanin cewar, an zabo mutum uku-uku daga kowace mazaba goma sha daya dake yankin.
Yana mai cewar, Karamar Hukumar ta yanke shawarar hakan ne domin bai wa dalibai damar karatu cikin sukuni.
Dr Muhammad Uba Builder, ya kara da cewar nan gaba kadan Karamar Hukumar za ta kara zabo wasu daliban dan tafiya manyan jami’o’i dake kasar nan.
A cewarsa, an kafa kwamati dan tantancewa daliban da suka cancanta.
A nasa jawabin Shugaban kwamatin tantance daliban kuma shugaban ma’aikata na yankin Yarima Musa, ya ce za su zabo daliban da suka cancata domin tura su makarantun da suka dace.
Ya kuma ya yabawa Shugaban Karamar Hukumar ta Birnin Kudu bisa namijin kokarinsa wajen daukar nauyin karatun daliban domin samun ingantacciyar rayuwa mai amfani a nan gaba.
Usman Mohammed Zaria
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
